IQNA

Al'ummar Barain na Gudanar Da Jerin Gwano Domin Saki Sheikh Ali Salman

23:54 - June 02, 2015
Lambar Labari: 3310739
Bangaren kasa da kasa, mutane da dama suka gudana da jerin gwano a yau a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain domin neman mahukuntan kasar da su gagaguta sakin Seikh Ali Salman.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Awifagh cewa, a yau dubban mutane ne suka gudana da zanga-zanga a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain domin neman mahukuntan kasar da su gagaguta sakin Seikh Ali Salman da suke tsare da shi saboda dalilai na siyasa. 

Ita ma a nata bangaren kungiyar kare hakkin bil-Adama kasa da kasa ta bukaci hanzarta sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman.

A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta fitar a jiya yana dauke da sanarwar cewa; Mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar Al-Wefaq kuma jagoran ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Tun a ranar 28 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2014 mahukuntan Bahrain suke tsare da Sheikh Ali Salman saboda furta rashin amincewarsa ga munanan matakan da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ke dauka kan ‘yan adawan Bahrain.

Har ila yau kungiyar ta bukaci gidan sarautar Bahrain da ta mutunta hakkin furta albarkacin baki da duk wani yunkurin ‘yan adawa ta lumana tare da kawo karshen dokokin da suka hana kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar.

3310563

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha