Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Al-wifagh cewa, babban malamin Addinin Musulunci na Kasar Bahrain Sheikh Isa Qasim ya ce; Kokarin da gwamnatin kasar ke yi na murkushe masu zanga-zangar lumana zai ci tura.
Shehin Malamin yana cewa; Murkushe Zanga-zangar ‘yan hamayyar kasar da mahuknta ke yi domin tilasta su mika wuya ga masu mulki, wani lamari ne da zai ci tura.
Da ya ke yin ishara da yadda jami’an tsaron kasar su ke amfani da karfi akan masu Zanga-zangar lumana ta neman kawo sauyi, Sheikh Isa Qasim ya ce; babu abinda zai karawa mutane idan ba karfin azama da hadin kai ba.
Kusan mako guda kenan da al’ummar kasar ta Bahrain su ke Zanga-zangar neman sakin daya daga cikin jagororin ‘yan hamayya da aka kama, wato sheikh Ali Salman. Zanga-zangar lumana da zaman lafiya a kasar Bahrain domin neman kawo sauyi ta shiga cikin shekara ta hudu.
Babban malamin ‘yan Shi’a na kasar Bahrain Ayatullah Isa Qasim ya kirayi al’ummar musulmi da su nesanci duk wani abin da zai haifar da rikici a tsakaninsu yana mai cewa babu wani abin da zai sanya makiya cimma manufarsu a kan musulmi kamar rikici da yaki a tsakaninsu.
Ayatullah Isa Qasim ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba inda ya ce makiya al’ummar musulmi suna ta kokari wajen haifar da yakin kabilanci da na basasa tsakanin musulmi da nufin rarraba kan musulmi don cu cimma bakar aniyarsu.
A cikin sanarwar Shehin malamin ya kirayi musulmin da su yi taka tsantsan kan makirce-makircen makiya wadanda suka jima suna dana musu tarko.
Haka nan kuma Shehin malamin ya kirayi gwamnatocin kasashen biyu da su yi kokarin sauke nauyin da ke wuyansu wajen karfafa al’ummominsu kana kuma su guji amfani da duk wata kalma ko kuma wani aiki da zai haifar da rikici da rarrabuwan kai tsakanin musulmin.
3310877