IQNA

Kaucewa Rashin Fahimtar Hakikanin Imam / Bayyana Sahihiyar Hanyar Imam (RA)

17:49 - June 05, 2015
Lambar Labari: 3311026
Bangaren siyasa, Jagoran juyin jya halin muslunci ya bayyana cewa Imam ya fayyace hakikanin hanya kuma dole ne a kauce ma duk abin da zai jawo rashin fahimtarsa domin kada a fada cikin kure.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jagora cewa, a safiyar Alhamis Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Ali Khamenei ya jagoranci taron tunawa da shekaru 26 da rasuwar marigayi Imam Khumaini, wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da aka gudanar a hubbaren marigayin da ke wajen birnin Tehran.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan gagarumin taro maras tamka, Ayatullah Khamenei ya bayyana tafarki da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin taswirar hanyar da ke cike da kyakkyawan fata ta al'ummar Iran, sannan kuma yayin da yake jaddada wajibcin fada da kokarin jirkitawa da kuma shafa kashin kaji ga hakikanin shaksiyyar marigayi Imam din, Jagoran cewa yayi: Dubi da idon basira cikin asalin tushen koyarwar marigayi Imam Khumaini, ita ce hanya guda daya tilo ta fada da kokarin shafa kashin kaji ga shaksiyyar mai girma Imam; wadannan koyarwar kuwa sun hada da: tabbatar da Musulunci na hakika da Annabi Muhammadu ya zo da shi da kuma yin watsi da Musulunci samfurin Amurka, dogaro da kuma yarda da alkawarin Ubangiji da rashin yarda da ma'abota girman kai, yarda da kuma imani da karfin mutane da kuma adawa da mika komai ga gwamnati, goyon baya da dukkanin karfi ga marasa galihu da kuma adawa da takama da iko, goyon bayan wadanda ake zalunta a duniya da kuma adawa a fili da azzaluman duniya, ‘yancin kai da kuma rashin amincewa da mulkin mallaka sannan da kuma jaddada wajibcin hadin kai.

A farkon jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da ranar 15 ga watan Sha'aban, wato zagayowar ranar da aka haifi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), inda ya ce batun bayyanar mai ceton al'umma a karshen zamani wani lamari ne da dukkanin saukakkun addinai suka yi imani da shi inda ya ce: Dukkanin mazhabobin Musulunci sun yi amanna da cewa wannan mai ceton zai fito ne daga zuriyar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa sannan kuma sunansa Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) inda su kuma ‘yan Shi'a bisa dogaro da karfafan hujjoji suka ce shi ne shi ne mai girma Imam Mahdi dan Imami na sha daya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana sanya fata cikin zukata a matsayin mafi girman siffar da batun dogaro da bayyanar Mahdi ta kebanta da ita inda ya ce: Hasken irin wannan imani da yarda (da bayyanar Mahdi) ne ya sanya kyakkyawan fata cikin zukatan ‘yan Shi'a a da kuma motsar da su a dukkanin zamunna da suka kasance cikin zalunci da babakere.

Yayin da kuma ya koma kan asalin jawabin nasa na yau, wanda shi ne kokarin da wasu suke yi na jirkita hakikanin shaksiyyar marigayi Imam Khumaini da kuma shafa masa kashin kaji, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Sabanin kokarin da wasu suke yi na takaita marigayi Imam ga zamaninsa, amma Mai girma Imam ya kasance wata alama ta gagarumin yunkuri da ya sauya tarihin na al'ummar Iran. Ko shakka babu jirkitawa da kuma shafa kashin kaji ga shaksiyyar marigayi Imam lamari ne da zai haifar da gibi cikin ci gaban wannan yunkuri. A saboda haka wajibi ne a yi taka tsantsan kan wannan lamarin.

Ayatullah Khamenei ya bayyana mahanga ta tunani, siyasa da zamantakewa ta marigayi Imam Khumaini, Allah Ya yi masa rahama, ta kasance wata taswirar hanya ga al'ummar Iran wajen isa ga manyan manufofinsu irin su tabbatar da adalci, ci gaba da kuma tsayin daka. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ci gaba da riko da wannan taswirar hanyar ba zai yiyu ba matukar ba a yi wa Imam ingantacciyar fahimta wacce ba a murguda ta ba.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wasu fitattun bangarori na rayuwar marigayi Imam da suka hada da bangare na fikihu, irfani da falsafa wanda ya ce hakan wata alama ce da take tabbatar da ayoyi daban-daban na Alkur'ani mai girma da suke siffanta masu jihadi na hakika a tafarkin Allah wadanda suka yi jihadi na hakika da kuma sauke nauyin da ke wuyansu.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A kokarinsa na haifar da gagarumin sauyi maras tamka a kasar nan da kuma duniyar musulmi, mai girma Imam Khumaini ya kawar da rubabbiyar tsarin sarauta na gado da kuma kafa wani tsari da kuma hukuma ta farko tun bayan farkon Musulunci wacce ta ginu bisa koyarwar Musulunci da dukkan karfinta, ya kuma yi jihadi a tafarkin Allah.

Jagoran ya bayyana jihadi (fada) da son zuciya da kuma neman kusaci da Ubangiji a matsayin wani lamari mai kammala jihadin marigayi Imam Khumaini a fagen siyasa, zamantakewa da tunani, hakan nan kuma yayin da yake ci gaba da bayanin bangarori daban-daban na tafarkin marigayi Imam Khumaini, Jagoran cewa yayi: Tunanin da ya sami damar haifar da wannan gagarumin sauyi, wani tunani ne da ya ginu bisa koyarwa ta tauhidi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tafiya da zamani a matsayin siffa ta biyu da tafarkin Imam Khumaini (r.a) ya kebanta da ita inda ya ce: Ta hanyar dogaro da tunaninsa, marigayi Imam Khumaini ya kasance mai gabatar da hanyoyin magance matsalolin da al'ummar Iran da sauran bil'adama suke fuskanta. Al'ummomi kuwa suna ganin tasiri da kuma kimar wadannan maganin matsalolin (da Imam yake gabatarwa). A saboda haka ne tafarkin Imam ya zamanto yake da matsayi da kuma yaduwa a tsakanin al'ummomi.

Jagoran ya bayyana rayuwa, yunkuri da motsi a matsayin wasu siffofin na daban da tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kebanta da su inda ya ce: Imam dai bai kasance kamar irin wasu masana da ‘yan bokon wadanda suka kware wajen dadin baki, to amma a fagen aiki kan sufuli suke.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana haifar da kumaji, yunkuri da kuma fata cikin zukatan al'ummar Iran a matsayin wasu daga cikin albarkokin riko da tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a) inda ya ce: Har ya zuwa yanzu akwai tazara mai girma tsakanin al'ummar Iran da manufofin da take son isa gare su, to amma abin da ke da muhimmanci shi ne cewa al'ummar Iran da matasanta sun ci gaba da tafiya a kan wannan tafarkin da dukkanin karfi da himmarsu.

Jagoran ya bayyana cewar ci gaban wannan tafarki ya damfara ne da ingantacciyar fahimtar shaksiyyar marigayi Imam da koyarwarsa. Daga nan sai ya ce: Jirgitar shaksiyyar Imam da tafarkin Imam, wani kokari ne na kawar da al'ummar Iran daga mikakkiyar hanyar da suke kai. Matukar aka mance ko kuma abin Allah ya kiyaye da gangan aka yi watsi da tafarkin Imam, to kuwa al'ummar Iran za ta cutu da kuma shan kashi.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin irin yadda ma'abota girman kan duniya da sauran masu takama da karfi suke sanya dukkanin fata da kwadayinsu wajen ganin sun mallake Iran a matsayin ta na kasa mai girma, arziki da kuma tasiri a yankin Gabas ta tsakiya, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wadannan ‘yan babakeren na duniya za su yi watsi da irin wannan kwadayin da ba a koshi din da suke da shi ne kawai a lokacin da al'ummar Iran suka sami irin ci gaba da kuma karfin da za su iya katse wannan kwadayin.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar ci gaba da kuma karfin al'ummar Iran yana cikin riko da kuma aiki da wadannan koyarwa ta marigayi Imam ne, Jagoran cewa yayi: Bisa la'akari da wannan lamarin ne muhimmancin hatsarin da ke cikin kokarin jirkita shaksiyyar Imam ke dada fitowa fili. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati, masana, tsoffin almajiran marigayi Imam, masoya tafarkin Imam da kuma dukkanin matasa su yi taka tsantsan da kuma kallon wannan lamarin da idon basira.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar kokarin gurbata shaksiyya da kuma tafarkin marigayi Imam Khumaini ne ba wai wani lamari ne na baya-bayan nan ba face dai wani lamari ne da aka yi jima ana yinsa tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci. Daga nan sai ya ce: Dukkanin kokarin makiya tun farkon juyin juya halin Musulunci da kuma a zamanin rayuwar Imam (r.a) shi ne sun bayyana wa duniya Imam a matsayin wani mutum mai kaushin hali maras tausayi.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Marigayi Imam Khumaini ya kasance mutum ne tsayayye mai jajurcewa a wajen tinkara ma'abota girman kai, to amma a daidai wannan lokacin kuma ya kasance ma'abocin tausayi da kauna da kankan da kai a gaban Allah da kuma bayinSa musamman raunanan cikin al'umma.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin da wasu a cikin Iran suke yi wajen jirkitar shaksiyyar Imam da tafarkinsa sun sani ko ba su sani ba, Jagoran cewa yayi: A lokacin rayuwar marigayi Imam (r.a), wasu mutane sun kasance duk wata maganar da ta yi musu dadi su kan zo su jingina ta ga Imam, alhali kuwa ba ta da wata alaka da Imam.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Bayan rasuwar marigayi Imam ma an ci gaba da hakan ta yadda hatta wasu ma suna bayyana Imam a matsayin mai riko da tafarkin sassauci ba tare da wani sharadi ba cikin dabi'unsa na siyasa, da tunani da kuma al'adunsa, alhali kuwa hakan babban kuskure kuma ba gaskiya ba ce.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar hanya guda kawai ta fahimtar shaksiyya da kuma tafarkin Imam da kyau ita ce fahimta da kuma sake dubi cikin koyarwa da kuma tunaninsa. Daga nan sai ya ce: Matukar ba a fahimci Imam ta wannan fagen ba, mai yiyuwa ne wasu su dinga bayyana Imam da kuma tafarkinsu dadai da irin zaukinsu.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar so da kaunar da mutane suke yi wa Imam, wani lamari ne da zai ci gaba da wanzuwa sannan kuma makiya sun gaza wajen kawar da hakan, Ayatullah Khamenei ya ce: A saboda haka ne batun kokarin jirkita shaksiyya da koyarwar Imam ya zamanto wani lamari ne mai hatsarin gaske wanda dubi cikin koyarwarsa da kuma tushen tunanin Imam lamari ne da zai hana faruwar wannan hatsarin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar ana iya gano tushen koyarwa da kuma tunanin marigayi Imam (r.a) ne cikin jawabansa tsawon shekaru 15 na gwagwarmaya Musulunci da kuma shekaru 10 bayan nasarar juyin juya halin Musulunci inda ya ce: Matukar aka hada wadannan koyarwa waje guda, to kuwa za a iya fitar da hakikanin shaksiyyar marigayi Imam Khumaini, yardar Allah ta tabbata a gare shi.

Kafin yayi karin haske kan muhimman tushen koyarwar marigayi Imam Khumaini guda bakwai, Ayatullah Khamenei yayi karin haske kan wasu lamurra masu muhimmanci cikin koyawa da kuma mahangar marigayi Imam (r.a).

1- A lokuta da dama marigayi Imam ya sha jaddadawa kan wadannan tushen ta yadda ma sun zamanto wani bangare na jawabansa.

2- Bai kamata a mai da wadannan tushen a matsayin wasu abubuwan da za a dinga zabansu ana magana kansu daidai da zaukin mutum ba.

3- Tushen koyarwar Imam ba kawai sun takaita cikin wadannan tushe guda bakwai ba ne, masana za su yi gudanar da bincike su ciro wasu siffofi da tushen na daban.

Daga nan kuma yayin da yake karin haske kan wadannan tushe guda bakwai da suka zamanto tushen koyarwa da mahangar marigayi Imam Khumaini, Jagoran cewa yayi: Tabbatar da Musuluncin Annabi Muhammadu (s.a.w.a) na hakika da kuma watsi da Musulunci samfurin Amurka daya ne daga cikin irin wadannan koyarwa na marigayi Imam. A koda yaushe Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kasance mai gabatar da Musulunci na hakika a gaban Musulunci samfurin Amurka.

Yayin da yake karin haske kan hakikanin wannan Musulunci samfurin Amurkan, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da wasu siffofi guda biyu, wato "Musuluncin da babu ruwansa da addini" da kuma "Musuluncin da aka bar shi a baya" daga nan sai ya ce: A koda yaushe Imam (r.a) ya kasance yana sanya mutanen da suke maganar wajibcin raba addini da rayuwa da dabi'un mutane da kuma mutanen da suke kallon addini da kallo na koma baya da rashin ci gaba a waje guda, wato dukkaninsu Danjuma ne da Danjummai.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar dukkanin wadannan sassa biyu na Musulunci samfurin Amurkan a koda yaushe sun kasance karkashin kulawa da kuma goyon bayan masu tinkaho da karfi na duniya da kuma Amurka ne, don haka sai ya ce: A yau ma Amurka da Isra'ila suna ci gaba da goyon bayan wadannan batattun kungiyoyin na Da'esh (ISIS) da Alka'ida da kuma kungiyoyin da a zahiri na Musulunci ne amma a hakikanin gaskiya sun jahilci karantarwar Musulunci na hakika.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A mahangar marigayi Imam, Allah Yayi masa rahama, Musulunci na hakika, shi ne dai Musuluncin da ya ginu bisa Alkur'ani da Sunna, wanda yake da fitacciyar mahangar da ta dace da zamani da kuma bigiren da ake, (yake da) masaniya kan bukatun al'ummar musulmi da ma sauran al'ummomi na duniya, ya fahimci hanyoyin da makiya suke bi, kana kuma ya tabbatar da kansa ta hanyar amfani da tafarki na ilimi da aka samo shi daga makarantun addini.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: A mahangar marigayi Imam (r.a), Musulunci irin na malaman fada da kuma Musulunci irin na ‘yan Da'esh, sannan a daya bangaren kuma Musulunci dan ba ruwanmu dangane da irin danyen aikin da Sahyoniyawa da Amurka suke aikatawa da kuma mika kai da fata ga manyan azzaluman duniya, a daya bangaren, dukkanin wadannan biyu tushensu guda ne, kuma abin yin watsi da su ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne mutanen da suke ganin kansu a matsayin mabiya Imam (r.a), su shata kan iyaka a tsakaninsu da daskararren Musulunci (da aka bar shi a baya) da kuma Musuluncin da babu ruwansa da addini (wanda ke yada cewa Musulunci ba shi da matsayi cikin rayuwar mutane).

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "dogaro da taimakon Allah da kuma yin imani da gaskiyar alkawarin Ubangiji bugu da kari kan rashin dogora da manyan ma'abota girman kai da masu tinkaho da karfi na duniya" a matsayin tushe na biyu na koyarwa da kuma tunanin marigayi Imam Khumaini (r.a), daga nan sai ya ce: A koda yaushe marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kasance mai riko da kuma gaskata alkawarin Ubangiji. A daya bangaren kuma bai taba yarda ko imani da alkawarin ma'abota girman kan duniya ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wannan sananniyar siffa da Imam ya kebanta da ita ce ya sanya a fili yake fadin mahangarsa ba tare da wani tsoro ko kwane-kwane ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da amsoshin da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya ke rubuta wa wasikun da wasu shugabannin kasashen duniya ma'abota girman kai suka rubuto masa, da bayyanar da mahangarsa a fili duk kuwa da cewa cikin girmamawa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Imam ya tabbatar da dogaro da Allah cikin zukatan al'ummar Iran, don haka al'ummar Iran suka zamanto ma'abota dogaro da Allah da kuma imani da taimakonsa.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan rashin komai kashin dogaro da ma'abota girman kai da kuma alkawarinsu da Imam yake da shi, Jagoran ya bayyana cewar: A halin yanzu a fili mun gani da kuma jin hakan a jikinmu sannan kuma mun fahimci mene ne dalilin da ya sanya ba a iya dogaro da alkawarin ma'abota girman kai ba. Don kuwa a tarurrukan bayan fage za su fadi wani abu na daban, a fili kuma su zo suna fadi da kuma aikata wani abin na daban.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar "dogaro da Allah da kuma rashin yarda da ma'abota girman kai" daya ne daga cikin tushen koyarwar marigayi Imam Khumaini. Daga nan sai ya ce: Koda yake hakan ba wai yana nufin katse alaka da duniya ba ne. Don kuwa akwai alaka irin wacce aka saba da ita sannan kuma wacce ta ginu bisa tushen girmama juna. To amma babu komai kashin yarda da ma'abota girman kai da ‘yan amshin shatansu.

"Imani da karfin mutane da kuma nesantar mika komai ga gwamnati" shi ne tushe na uku daga cikin tushen koyarwar marigayi Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei yayi ishara da shi cikin jawabin nasa.

Haka nan yayin da yake jaddada cewar a koda yaushe marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kasance mai dogaro da karfi na jama'a cikin lamurra daban-daban na tattalin arziki, aikin soji, gina kasa, isar da sako sannan kuma uwa uba cikin zabubbuka, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Tsawon shekaru 10 na rayuwar marigayi Imam bayan nasarar juyin juya halin Musulunci wanda shekaru takwas cikinsu lokaci ne na kallafaffen yaki, an gudanar da kimanin zabubbuka guda 10 sannan kuma babu koda sau guda da aka sauya lokacin gudanar da zaben. An gudanar da su a daidai lokacin da aka tsara. Don kuwa Imam (r.a) ya kasance mutum ne mai girmama ra'ayi da kuma mahangar mutane da dukkanin ma'anar wannan kalma ta girmamawa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Hatta a wasu lokuta mai yiyuwa ne a samu cewa mahangar Imam da kuma ta mutanen ta bambanta, to amma duk da haka Imam ya kasance mai girmam ra'ayin mutanen.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawaban Imam inda a lokuta da dama ya ke bayyana mutane a matsayin ma'abotan kasa sannan shi kuma a matsayin mai musu hidima, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan kalami wata alama ce da ke nuni da matsayin da mutane suke da shi cikin tunani da kuma ra'ayin marigayi Imam. Tabbas su ma mutane a nasu bangaren sun nuna jinjinawarsu ga hakan, ta yadda a duk wata ishara da Imam zai yi, nan take mutane da dukkanin karfinsu za su kasance a wajen.

Don haka sai Jagoran ya ce: Akwai alaka ta so da kauna a tsakanin mutane da Imam. Imam ya kasance mai kaunar mutane, su ma haka sun kasance suna kaunarsa.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi nuni da wani tushe na daban daga cikin tushen koyarwar ta Imam inda ya ce: Dangane da batutuwa na cikin gida ma, marigayi Imam ya kasance mai tsananin goyon bayan talakawa da raunana, sannan kuma ya kasance mai tsananin adawa da nuna fifiko na tattalin arziki tsakanin al'umma.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kasance mai tsananin goyon bayan tabbatar da adalci na zamantakewa a tsakanin al'umma, Ayatullah Khamenei ya bayyana wannan lamarin a matsayin daya daga cikin batutuwan da marigayi Imam ya fi nanatawa cikin jawabansa sannan kuma daya daga cikin manyan tushen koyarwarsa. Jagoran ya ci gaba da cewa: A bangare guda Imam ya kasance mai kira zuwa ga wajibcin tumbuke tushen talauci da rashi a tsakanin al'umma, sannan a bangare guda kuma ya kasance mai jan kunnen jami'an gwamnati dangane da almubazzaranci, son jin dadin rayuwa da kuma ado na nuna kai.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan jaddadawar da Imam yake yi wa jami'an gwamnati kan dogaro da talakawa da raunanan cikin al'umma, Jagoran cewa yayi: Marigayi Imam ya sha fadin cewa wadannan talakawa da fakiran su ne dai suka kasance a fage ba tare da nuna damuwarsu bisa matsaloli da wahalhalun da suke ciki ba, alhali su kuwa masu shi su suka fi nuna raki kan matsalolin da aka fuskanta.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin tushe na biyar na koyarwar marigayi Imam Khumaini, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A bangaren kasashen waje ma, Imam a fili yake bayyana adawarsa da "sansanin ‘yan mulki mallaka da ma'abota girman kan duniya", sannan kuma babu wani noke-noken da yake yi wajen nuna goyon bayansa ga wadanda ake zalunta.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa Imam (r.a) ba ya zama inuwa daya da ma'abota girman kai, Ayatullah Khamenei ya bayyana Kalmar ‘Babbar Shaidaniyya' da Imam yayi amfani da ita kan Amurka a matsayin wani hangen nesa mai ban mamaki inda ya ce: Abubuwa da ma'anonin da suke cikin wannan kalma ta ‘Babbar Shaidaniyya' suna da yawan gaske. Saboda kuwa a lokacin da aka ba wa wani mutum lakabin Shaidan, wajibi ne ya zamanto duk wata mu'amala da za a yi da shi ta kasance karkashin wannan siffa ta Shaidan ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: har zuwa karshen rayuwarsa, Imam ya kasance mai irin wannan ra'ayin kan Amurka. Ya kasance yana amfani da wannan kalmar ta "Babbar Shaidaniya" a kan Amurka. Yayi amana sama da kasa da hakan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A daya bangaren kuma, tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci wasu ba su lura da rawar da Amurka ta taka wajen karfafa gwamnatin dagutu da aka kifar a kasar nan ba. A saboda haka ne suka yarda da ci gaba da kasantuwar Amurka a kasar nan kai har da da ci gaba da ayyukanta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar wannan lamarin shi ne tushen sabanin da ya kunno kai tsakanin Imam da gwamnatin rikon kwarya a shekarun farko-farko na nasarar juyin juya halin Musulunci inda ya ce: Wadannan mutane ba su fahimci cewa idan har aka sake ba wa Amurka dama, to kuwa za su cutar da al'ummar nan. To amma shi Imam ya fahimci hakan. A bisa hakan ne ya kai daukar matsayarsa. Matsayar da Imam ya dauka dangane da mamaye "Shekar Leken Asiri" (ofishin jakadancin Amurka) da (daliban mabiya tafarkin Imam) suka yi ya ginu ne bisa wannan mahangar.

Jagoran yayi ishara da wasu abubuwan da suke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya a shekarun baya-bayan nan da kuma yadda wasu suka dogara da Amurka da yadda Amurkan ta ha'ince su inda ya ce: A bisa wannan mahanga tasa ne, marigayi Imam Khumaini ya kasance yana bayyanar da mahangarsa da kan Amurka da cibiyoyinta na tsaro da kuma na siyasa; a bangare guda kuma da bayyanar goyon bayansa ga al'ummomin da ake zalunta musamman al'ummar Palastinu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce bisa irin wannan mahanga ta Imam ne ya kamata a kalli lamurran da suke faruwa da kuma yin sharhi kansu inda ya ce: A yau din kamar yadda muke adawa da wuce gona da iri da zaluncin da kungiyar Da'esh suke yi a Iraki da Siriya, haka muke adawa da zaluncin ‘yan sandan Amurka a cikin kasar (Amurka). Muna ganin dukkanin wadannan dabi'u biyun a matsayin Danjuma da Danjummai ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Haka nan kamar yadda muke adawa da killacewar zalunci da aka yi wa al'ummar Gaza, haka muke adawa da hare-haren bama-baman da ake kai wa mutanen Yemen marasa kariya. Haka nan kuma muke adawa da matsin lambar da ake yi wa mutanen Bahrain da kuma hare-haren da jiragen yakin Amurka marasa matuka suke kai wa kan al'ummomin kasashen Afghanistan da Pakistan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa bisa riko da koyarwar marigayi Imam Khumaini za su ci gaba da goyon bayan wadanda aka zalunta da kuma nuna adawa da azzalumai. Don haka sai ya ce: A bisa wannan dalilin ne ya sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya matsalar Palastinu ta zamanto matsalarta. Ba za ta taba yin watsi da wannan lamarin ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Batun Palastinu wani fage ne jihadi na wajibi ne na Musulunci, don haka babu wani abin da zai taba raba mu da batun Palastinu. Ayatullah Khamenei: Mai yiyuwa ne wasu a fagen Palastinu su gaza wajen sauke nauyin da ke wuyansu, to amma abin da muka yi amma da shi da kuma goyon bayansa shi ne mutane da kuma jihadin al'ummar Palastinu.

"Tabbatar da ‘yancin kai da kin amincewa da mulkin mallaka" shi ne tushe na shida na koyarwar marigayi Imam Khumaini da Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da shi.

Yayin da yake ishara amannan din da marigayi Imam yayi da batun ‘yancin kai da kuma kore mulkin mallakan masu tinkaho da karfi na duniya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa da dama daga cikin irin ayyukan da makiya suke yi da suka hada da barazana da takunkumin da suke sanya wa al'ummar Iran suna yin hakan ne duk dai da nufin dakile kaifin wannan tushe da aka rika. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Makiya dai suna adawa ne da ‘yancin kan kasar nan. A saboda haka wajibi ne kowa da kowa yayi taka tsantsan da kuma fahimtar manufar makiya.

Batun "hadin kai na kasa da kuma fada da makircin makiya na rarraba kan al'umma" shi ne tushe na karshe na koyarwar marigayi Imam Khumaini da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da shi.

Jagoran ya bayyana rarrabuwan kai na mazhaba da na kabilanci a matsayi daya daga cikin bakaken siyasa da manufofin makiya, don haka sai ya ce: Don fada da wannan makircin, tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci marigayi Imam Khumaini ya ba da himma sosai kan batun hadin kai na kasa da kuma fahimtar juna tsakanin al'ummar Iran.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ci gaban wannan siyasa ta rarraba kan al'umma da makiya suke yi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana haifar da sabani a duniyar musulmi a matsayin daya daga cikin tushen siyasar ma'abota girman kai da kuma Amurka inda ya ce: Don fada da wannan makircin, mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai wata mahanga ce ta ‘gina al'umma' da kuma son kafa al'umma musulma. A saboda haka ne irin mu'amalar da Iran take yi da ‘yan'uwa ‘yan Shi'a na kungiyar Hizbulla (ta kasar Labanon) irin wannan mu'amalar take yi da ‘yan'uwanmu na Palastinu wadanda ‘yan Sunna ne.

Ayatullah Khamenei ya bayyana shigo da maganar "Kusurwoyin Shi'a" da wasu kaskantattun ‘yan amshin shatan Amurka da kuma irin goyon bayan da Amurka take ba wa kungiyoyin ‘yan ta'adda irin su kungiyar Da'esh a Iraki da Siriya a matsayin wani misali na ayyukan ma'abota girman kan duniya wajen rarraba kan al'umma inda ya ce: Wajibi ne kowa da kowa, Shi'a ne ko Sunna ya fahimci wannan lamarin, don kada ya fada tarkon makiya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Irin sunnancin da Amurka take goyon baya, haka nan Shi'ancin da ake isar da shi zuwa ga duniya daga London, dukkanin wadannan biyun ‘yan'uwan Shaidan ne sannan kuma ‘yan amshin shatan ma'abota girman kai da kuma kasashen yammaci ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Makiya dai suna harin tushen kasantuwar Musulunci ne. A saboda haka wajibi ne dukkanin kabilu da mazhabobi su hada hannunsu waje guda wajen ganin ba su bari makiya sun sami kutsawa da tasiri a duniyar musulmi ba.

Ayatullah Khamenei dai ya ce irin wadannan koyarwar ta marigayi Imam Khumaini (r.a) su ne suka sanya zukatan al'umma komawa gare shi da kuma kaunarsa. Don haka sai ya ce: Tabbas tushen koyarwar marigayi Imam ba zau takaita ga wadannan (abubuwan) da muka ambato ba. A saboda haka masana za su yi ci gaba da gudanar da bincike. Sai dai kuma bai kamata wani ya dinga jingina wa Imam abin da shi ya yarda da shi ba. Face dai wajibi ne dukkanin abubuwan da za a fadi ya zamanto yana da bisa tushen koyarwar ta Imam ne.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wani lamari mai muhimmanci inda ya ce: Wajibi ne kowa ya san cewa manufar makiya ita ce komar da kasar nan baya zuwa ga lokacin sarakuna ba tare da wani sharadi ba. Dukkanin ihu, dariya, alkawari da kuma barazanar da suke yi, duk suna yin su ne don cimma wannan manufar.

Ayatullah Khamenei ya ce: Makiya suna adawa ne da Musulunci, don kuwa Musulunci babban karfi ne wajen fada da wannan makircin. Suna adawa da al'ummar Iran, saboda al'ummar Iran sun tsaya kyam a gabansu ne tamkar wani dutse.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Makiya suna adawa sosai ne da duk wanda tsayin dakansa ya fi tsanani. Su din nan suna adawa da muminai ‘yan kungiyar Hizbullah masu riko da addini da sauran cibiyoyi na juyin juya halin Musulunci ne saboda sun san cewa wadannan mutanen sun kasance tamkar wani dutse ne wajen hada tasirin makiya.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci dai sai da Hujjatul Islam wal muslimin Sayyid Hasan Khumaini, jikan marigayi Imam Khumaini kuma mai kula da haramin marigayi Imam din ya gabatar da jawabin barka da zuwa ga mahalarta wannan taron. Inda a jawabin da ya gabatar din yayi ishara da abubuwan da suke faruwa a kasashen Iraki, Siriya, Yemen da Bahrain inda ya zargin gwamnatocin da aka bar su a baya na yankin nan a matsayin wadanda suke da hannu cikin rura wannan wutar.

Sayyid Hasan Khumaini ya kara da cewa: A halin yanzu dai kasashen musulmi suna fuskantar wani irin yanayi mai sosa rai wanda wadansu mutane da suke da adawa da kiyayya da Musulunci suka haifar da su.

Sayyid Hasan Khumaini ya ci gaba da cewa: Wasu mutane masu kaushin hali suna ci gaba da cutar da dukkanin ci gaba na Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo da shi, suna zubar da jinin mutane da kuma shafa kashin kaji ga addinin Musulunci karkashin goyon bayan ‘yan kasashen waje da kuma sahyoniyawa.

Sayyid Hasan Khumaini ya jaddada cewar kasar Iran dai kasa ce ta marigayi Imam Khumaini, don haka sai ya ce: Duk wanda ya kalli al'ummar Iran, zai gane cewa al'ummar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan dakarun kasa (Ayatullah Khamenei) ba za su taba barin wani ya wuce gona da iri kan wannan kasar, sannan kuma za su ci gaba da kokari wajen kare dukkanin hurumi da kuma mutumcin kasar nan.

3310875

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha