Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-shuruq Online cewa, Muhammad Isa ministan kula da harkokin addini na kasar Aljeriya ya bayyana cewa sun aike da gayyata zuwa ga kasashe 66 kuma kasashe 10 daga cikinsu ba mambobin kungiyar kasashen musulmi ba ne wato Russia, Vanada, India da kuma Philipines, dangane da shirye-shiryen gudanar da gasar harda da karatu da kuma tajwidin kur’ani mai tsarki a kasar Aljariya a cikin watan Ramadan mai kamawa.
Ya ce ya zuwa ynzu dai halartar kasashe 45 daga cikin wadannan ya kasashe ya tabbata, yayin da sauran kuma ake ci gaba da jiran amsar da za su bayar dangane ko za su samu halartar wannan gasa da za a gudanar a cikin watan na azumi mai kamawa.
Dangane da masu halartar gasar kuwa, an sanya shekaru maza ya zama daga shekara 20 ne zuwa shekaru 25 na wadamnda za su halartaci wannan gasa domin karawa da juna.
Daga karshe kuma za a fitar da mutane 10 da za su kai ga mataki na karshe, wadanda za su kara da junansu, daga nan kma za a ci gaba da fitarwa har zuwa mataki na uku da kuma na biyu zuwa na daya, wadanda dukkanisu za su samu kyautuka na nuna kwazo.
3310879