Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, ministan harkokin wajen kasar Lebanon Jubran Basil ya bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce take amfana da rikicin shi’a sunna a tsakanin al’ummomin larabawa da kuma musulmi.
Ministan na Lebanon ya ce babu batun banbancin mazhaba a cikin batun yaki da ta’addanci, kuma hankoron da wasu suke yi domin kawo wanann batua yakin da ake yi da ‘yan ta’adda, hankoro ne kawai na neman samun shia a wajen gwamnatin yahudawan.
Dangane da abin da yake faruwa a cikin kasar ta Lebanon kuwa ministan ya bayyana cewa wajibi ne a kan kowane mutum ya bayar da gudunmawarsa domin tababtar da cewa an yaki yan ta’adda gadan-gadan a duk inda suke a cikin fadin kasar.
Ya kara da cewa wajibi ne ga duk wani dan kasa na gari ya mara baya ga sojojin kasar ta Lebanon ga kokarin da suke yin a yaki da ‘yan ta’adda, kuma goyon bayan rununar sojin kasar ba goyon bayan wani bangare ba ne, domin kuwa a cikin sojoji a kwai musulmi da dukaknin bangarorinsu, haka nan kuma akwai kiristoci da dama duk suna aiki tare domin kare kasa.
3311158