IQNA

Zantawa Da Musulmi Ya Canza Mani Akida Dangane Da Muslunci

22:12 - June 07, 2015
Lambar Labari: 3311884
Bangaren kasa da kasa, A makon da ya gabata Jasin Leger ya halarci zanga-zangar kiyayya da addinin mulsunci a cikin jahar Arizona ta kasar Amurka bai tsammanin cewa zai samu canji tunani kan akidarsa ba cikin karamin lokaci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muslim Global World cewa, wani mutum mai suna Jason Leger dan kasar Amurka da ke tsananin gaba da addinin muslunci, wanda ya halarci jerin gwanon kin jin muslunci a makon da ya gabata a jahar Arizona, ya bayyana cewa ya samu sauyin tunani a lokaci guda dangane da yadda yake kallon muslunci, bayan da ya je wani masallaci kuma ya tattauna da wasu musulmi dangane da addininsu, inda ya ce hakika ya fahimci cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da ke koyar da dan adam jin kai da kyawawan dabi'u.

Wadanda suka gudanar da wannan jerin gwanoo sun nuna wasu daga cikin zane-zane na batunci ga manzon Allah (SAW) da kuma addinin muslunci a lokacin da suke gangamin, duk da sunan yancin fadar albarkacin baki, wanda gwamnatin kasar ta yarje musu da cewa suna iya yin hakan a duk lokacin da suka ga dama.

Bayan gudanar da wannan zanga-zanga, wasu daga cikin kungiyoyin farar hula da suke rajin kare hakkokin yan adam sun kirayi wani gangami a cikin jahar Arizona domin yin Allawadai da duk wani yunkuri na nuna kyama ga musulmi ko wane bangare na al’ummar kasar saboda addininsu ko kuma wata akidarsu.

Haka nan kuma mabiya addinai da daman a kasar ta Amurka suna mince da bayanin kngoyoyin kare hakkokin al’umma musamman ma marassa rinjaye a kasar ta Amurka, wanda musulmi suna ciki, wadanda kuma ake nuna musu banbanci da tsananin gaba da wariya saboda addininsu.

3311408

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha