IQNA

An Bude Wata Cibiya Ta Musulunci A Jamus Ta Masu Fafutuka Na Bahrain

22:34 - June 09, 2015
Lambar Labari: 3312688
Bangaren kasa da kasa, an bude wata sabuwar cibiya ta masu gwagwarmaya da zaluncin mahukuntan kasar Bahrain mazauna kasar Jamus domin gudanar da harkokinsu a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na masu fafutuka cewa, a jiya ne aka bude wata sabuwar cibiya ta masu gwagwarmaya da zaluncin mahukuntan kasar Bahrain mazauna kasar Jamus domin gudanar da harkokinsu na addini da kuma neman sauyi.

Ali Mushaima daya daga cikin masu gwagwarmaya a Bahrain wanda a halin yanzu yake zaunea  kasar Jamus, shi ne ya jagoranci bude wannan cibiya, ya kuma bayyana cewa babbar manufar yin hakan it ace samar da wani wuri wanda za su rika gudanar da harkokinsu a kasar ta Jamus cikin yanci.

Ya ci gaba da cewa da dama daga cikin yan gwagwarmayar suna zaune  akasar Jamus ne bayan da aka kore su saboda ra’ayoyinsu na siyasa daga kasarsu ta haihuwa ba taree da wani hakki ba, inda ya ce za su yi amfani da wannan damar wajen kara bayyana wa duniya halin da suke ciki.

Azzaluman mahukuntan kasar Bahrain e sun jima suna yin amfani da karfi wajen murkushe duk wani wanda ya nuna musu rashin amicewarsa da zalincinsu, tare da neman hakkokinsa na dan kasa.

Wasu daga cikin masana yan kasar Bahrain masu fafutuka sun gudanar da jawabi a yayin bude wannan cibiya a kasar ta Jamus.

3312456

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha