IQNA

An Keta Alfarmar Kur’ani A Masalalcin Alkhiaf Na Kasar Bahrain

23:41 - June 11, 2015
Lambar Labari: 3313264
Bangaren kasa da kasa, an keta alfarmar alkur’ani mai tsarki da kuma littafan adduoi a masallacin mabiya tafarkin shi’a na Alhaifa kasar Bahrain.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa a safiyar yau an ballae kofifin masallacin an shiga an karya dukaknin abubuwan daka kafa kafin shiga a cikinsabayan kuma an keta wasu daga cikin littafan da ke kisan da suka hada da kwafin kur’ani mai tsarki da kuma adduoi.

Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sun bayyana cewa an kai harin kafin lokacin sallar asubahi wato a cikin dare, da nufin yin tsokana kan mabiya mazhabar shi’a na kasar, amma dai an dauki matakai bin kadun lamarin ta hanyoyin da suka dace.

Yan shi’a  kasar ta Bahrain suna nuna fargaba dangane da abin ka iya samunsu, musamman ma ganin abin da ya faru na kai harin ta’addanci a kan yan uwansu a masallacin Dammam na kasar Saudiyya, inda aka kai harin kunar bakin wake tare da kashe masallata, ganin cewa yanzu haka masautar khalifa ta rusa masallatai kimanin 38 na su a kasar.

Da dama daga cikin mutanen yankin na kira da akafa kwamitin wanda zai ido kan ayyukan masallatai da kuma kare daga ayyukan ta’addanci.

3313218

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha