Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, Robert Colvel shugaban kwamitin kare hakiin bila adama na majalisar dinkin duniya ya fitar da wata wasika da ya rubuta zuwa ga mahukuntan Bahrain a a cikin watan Janairu da ke neman su gaggauta sakin Sheikh Ali Salman domin dukkanin abubuwan da ake tuhumarsa ba su da tushe.
Y^a ci gaba da cewa sun bi kadun dukkanin abubuwan da mahukuntan Bahrain suka fada dangane da tuhumar da ske yi wa sheikh Ali Salman, amma babu ko daya daga cikinsu da yake gaskiya, kuma ana tsare da shi ne kawai saboda ra’ayinsa na siyasa, da ke neman ayi adalci da gaskiya a cikin sha’anin mulkin kasar.
Mahukuntan Bahrain wadanda ke kan gaba wajen yi kasashen yammacin turai amshin shata a yanking abas ta tsakiya suna cin karensu babu bababka akan al’ummar kasar da ke neman a yi a dalci a cikin harkokin mulkin kama karya da ake yi a kasar karkashin mulukiyya.
Abin mamaki shi ne yadda kasashen turai suka yi gum da bakunansu kan dukkanin wannan ta’asa da mahukuntan kasar ta Bahrain suke tafkawa kan al’ummar kasar, da hakan ya hada da shugaban babbar jam’iyyar mafi girma a kasar sheikh Salman, wand ake tsare da shi saboda dalilai na siyasa.
3313444