IQNA

Jagororin Musulmin Birtaniya Sun Nuna Rashin Gamsuwa Da Karuwar Kyamar Musulmi A Kasar

23:54 - June 17, 2015
Lambar Labari: 3315778
Bangaren kasa da kasa, jagororin mabiya addinin muslunci a kasar Birtaniya sun nuna rashin gamsuwarsu da abin da suka kira rawar da gwamnatin kasar ke takawa wajen kyamar muslunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IBTimes cewa, wasu daga cikin jagororin mabiya addinin muslunci a kasar Birtaniya sun nuna rashin gamsuwarsu da abin da suka kira rawar da gwamnatin kasar ke takawa wajen kyamar muslunci a kasar wadda ke mabiya addinin kirista masu rinjaye.

 

Daga cikin irin abubuwan da muslmin suke kokawa  akansa kuwa har da yadda ake ci gaba da kara samun kungiyoyin mutanen da suke bayyana gabarsu karara dangane da addinin muslunci, kuma sukan cutar da musulmin asar a cikin mu’amala kamar yadad sukan ci zarafinsu ta hanyar kafofin yada labarai da sadarwa.

Duk da hakan mahukuntan Birtaniya suna bayyana hakan amatsayin yancin fadar albarkacin baki da kuma bayyana ra’ayi, dk kuwa da cewa ana cin zarafin musulmin ne da suna addininsu da kuma akidarsu, wanda hakan ya sabawa dukaknin dokoki na kasar baki daya.

 

Domin kuwa bisa dokar kowa yana ikon ya yi addininsa cikin yanci a kasar ba tare da wani ya takura masa ba, kamar yadda yake da hakkin ya shigar da kara idan wani ya ci zarafinsa saboda addininsa.

3315168

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha