Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a yammacin Laraba Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da firayi ministan kasar Iraki Dakta Haidar Al-Ibadi da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa. A yayin ganawar Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana taka tsantsan wajen kare hadin kai na kasa da kuma na siyasa a tsakanin al'ummar Irakin a matsayin wani wajibi, haka nan kuma yayin da yake magana kan jaruntakar da matasan kasar Irakin suke nunawa a fadar da ake yi da ‘yan ta'adda a kasar, Jagoran cewa yayi: Ko shakka babu matsayin da dakarun sa kai na kasar Irakin suke da shi lamari ne da zai taimaka wajen ci gaban kasar a bangarori daban-daban.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa tsayin dakan al'umma da kuma gwamnatin Iraki wajen tinkarar ‘yan ta'addan kasar wani lamari ne da zai lamunce tsaron kasashen da suke yankin, Jagoran cewa yayi: Daya daga cikin siffofi masu muhimmanci da al'ummar Iraki suke da ita wanda kuma take ci gaba da bayyana a fagen yakin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta'adda a kasar, ita ce jaruntaka da kuma azama da karfin da dakarun sa kai na al'umma da kuma kabilun kasar suke da shi wajen fada da makiya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana bayyanar ‘yan ta'adda a kasar Irakin a matsayin wani lamari mai wucewa inda ya ce: Irin gagarumin karfin da dakarun sa kai na al'umma suke da shi, wata mabubbuga ce abar dogaro da ita a bangarori daban-daban ba wai kawai a fagen daga ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tsawon tarihin al'ummar Iraki shin a baya ne lokacin mulkin mallakan Ingila ko kuma a halin yanzu irin son mulki da nuna karfi na Amurka, babu wani lokaci da wadannan mutanen masu fatan sharri ga al'ummar Iraki suka yi maraba da bayyanar al'umma a fagen daga. A saboda haka wajibi ne a kiyaye wannan babban jari na al'umma da ake da shi.
Jagoran ya bayyana kokarin kawar da tushen hadin kai na kasa da kuma na siyasa a kasar Iraki a matsayin daya daga cikin manyan manufofin kasashen yammaci a kasar ta Iraki inda ya ce: Wajibi ne a yi fada da wannan makirci cikin taka tsantsan, sannan kuma kada a taba bari a raunata hadin kan da ke tsakanin Shi'a da Sunan da Kurdawa da Larabawa a kasar Irakin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan hadin kan kungiyoyi kasar Iraki ma'abota gwagwarmaya da juyin juya hali. A saboda haka wajibi ne jami'an kasar Iraki su yi taka tsantsan dangane da kokarin rarraba kan al'ummar Irakin da makiya suke kokarin yi.
Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa tsaro da kuma ci gaban kasar Iraki, yana a matsayin tsaro da kuma ci gaban kasar Iran ne, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Amurkawa dai a bangare guda suna so ne su dinga dibar man fetur din kasar Iraki kamar yadda suke yi a wasu kasashen yankin, a bangare guda kuma suna so su ci gaba da tilasta wa al'ummar kasar abubuwan da suke so kamar yadda suke yi a baya. To amma bai kamata a bari hakan ta faru ba.
Sannan kuma yayin da yake sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga gwamnatin kasar Irakin, Jagoran cewa yayi: Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan da take ba wa gwamnati da kuma al'ummar Iraki.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin karimcin da al'ummar Iraki suka nuna wa masu ziyarar Arba'in na Imam Husain (a.s) a matsayin daya daga cikin siffofi masu kyau da al'ummar Iraki suke da ita, inda ya ce: A irin wannan duniya ta mu ta yanzu da ta abin duniya a gaba, lalle irin wannan mu'amala mai kyau wani lamari ne mai muhimmancin gaske. Alal hakika har ya zuwa yanzu ba a gama fahimtar daukakar da al'ummar Iraki suke da ita ba.
Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Irakin Dakta Haidar Al-Abadi wanda mataimakin shugaban kasar Iran Malam Jihangiri yake wa jagoranci, ya bayyana tsananin farin ciki da jin dadinsa da wannan ganawar. Har ila yau kuma yayin da yake bayyana cewar irin goyon bayan da Iran take ba wa Iraki a matsayin wani lamari da ke nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashe biyun, Dakta Al-Abadi cewa yayi: Makiyan al'ummar Iraki sun tattara karfinsu waje guda don haifar da sabani da rarrabuwan kai na kabilanci da kuma mazhaba tsakanin al'ummar Irakin. To amma gwamnati da al'ummar Iraki sun kuduri aniyar fada da wannan makircin da kuma kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar babu wani bambanci tsakanin dan Shi'a da dan Sunna a wajen ‘yan ta'adda masu kafirta musulmi na kasar Iraki da na Siriya, firayi ministan na Iraki cewa yayi: Irin tsayin dakan da gwamnati da kuma al'ummar Iraki suka yi ne ya hana ci gaba da yaduwar ‘yan kungiyar Da'esh zuwa sauran kasashen yankin nan. To amma fada da wadannan ‘yan ta'addan yana bukatar hadin kan kasashen yankin nan.
Daga karshe Dakta Haidar al-Abadi ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da irin taimakon da take ba wa gwamnati da kuma al'ummar Iraki wajen fada da ‘yan ta'adda.
3315760