IQNA

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da Tsare Sheikh Ali Salman

23:49 - June 19, 2015
Lambar Labari: 3316040
Bangaren kasa da kasa, hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa da ke mazauni a Geneca ta yi kakakusar suka dangane da tsare sakataren jam’iyyar Wifaq Bahrain Sheikh Ali Salman.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Alwifaq cewa, Tara Agridi shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta kasa tana cewa, sn yi Allawadai da abin da mahukuntan Bahrain suke yi na cin zalun kan sheikh Ali Salman sakataren jam’iyyar siyasa ta Alwifaq, tare da yin kiran a gaggauta sakinsa ba tare da wani bata lokaci ba.
Kwararru kan harkokin shari’a da kare hakkokin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa matuka dangane da irin matakan da masarautar kasar Bahrain take dauka wajen murkushe ‘yan adawar siyasa a kasar, musamman ma tun bayan kame madugun adawa a kasar kuma babban sakaraen jam’iyyar adawar siyasa mafi girma a kasar Sheikh Ali Salman.

Mahukuntan na Bahrain dai sun kame Sheikh Ali Salman tun ranar ashirin da takwas ga watan disamban shekara da ta gabata, bisa hujjar cewa za su gudanar da bincike ne a kansa, amma tun daga lokacin suka saka a gidan kaso suna masu tuhumarsa da cewa yana kokarin kifar da masarautar kasar.

 

A cikin wani bayani da kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan wannan lamari a jiya, sun bayyana cewa dukkanin abin da masarutar Bahrain ke tuhumar Sheikh Ali Salman da shi kage ne na siyasa, kuma haka baya rasa nasaba da yunkurin da gidan sarautar kasar ke yi na murkushe mabiya mazhabar shi’a wadanda su ne kashi 86% na al’ummar kasar Bahrain, tare da nisantar da su daga duk wani sha’ani na siyasa ko tafiyar da mulki a kasar.

Tun a cikin Fabrairun shekara ta dub biyu da sha daya ne al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da gangami da jerin gwano domin neman a gudanar gyaran fuska dangane da yadda ake tafiyar da sha’anin mulki a kasar, inda suka bukaci sarki ya ci gaba da zama kan kujerarsa, amma a baiwa jama’a damar su zabi ‘yan majlaisar dokoki, ta yadda majalisar za ta zabi Firayi minista da kanta wanda zai kafa majalisar ministoci, kuma baiwa majalisar dama kafa kwamitin tsara kundin tsarin mulkin kasa wanda zai yi la’akari da hakkokin kowane bangare a kasar.

 

Maimakon yadda tsarin kasar yake na mulukiyyah, inda sarki shi ne wuka shi ne nama a komai, shi ne ke zabar Firayi minista da ministoci da ‘yan majalisa daidai da ra’ayinsa, ta yadda al’umma ba su da hakki a cikin hakan, bugu da kari kuma dukkanin mukamai a kasar mutane masu alaka da gidan sarautar ne ke rike da su, sauran jama’ar kasar kuma sun zama ‘yan kallo.

Bugu da kari kan hakan kuma al’ummar kasar Bahrain sun bukaci da a rika raba arzikin kasar bisa adalci, maimakon yadda lamarin yake  a halin yanzu, baya ga dabaibaye sha’anin mulki da siyasa, hatta ma arzikin kasar na sarki da ‘yayan sarauta da masu alaka da su ne kawai.

Maimakon yin nazari dangane da wannan kira na al’umma, masarautar Bahrain ta gayyaci dubban sojoji daga Saudiyya da Jordan da kuma Hadaddiyar daular larabawa domin murkushe masu yin wannan kira, kuma tun daga lokacin da aka fara boren shekaru hudu da suka gabata ya zuwa yanzu, masarautar Bahrain tare da taimakon wadannan kasashe, sun kashe tare da jikkata dubban fararen hula da suka hada da maza da mata da kananan yara, tare da cin zarafin jama’a da rushe wuraren ibada da cibiyoyin ilimi.

3315961

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha