IQNA

Isra’ila Ta Hana Palastinawa Zuwa Salla A Masallacin Aqsa

23:59 - June 25, 2015
Lambar Labari: 3318539
Bangren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta hana palastinawa kimanin 500 daga yankin Gaza zuwa sallar Juma’a ta biyu a cikin watan Ramadan mai alfarma a masallacin Aqsa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, a yau jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ta hana daruruwan palastinawa daga yankin Gaza zuwa sallar Juma’a ta biyu a cikin wannan wata mai alfarma a masallaci mai alfarma.

Adadin palastinawa da aka hana zuwa sallar sun kai kimanin 500 daga yankin zirin Gaza, yayin da kuma sauran wadanda suke yankunan gabacin birnin da gabar yamma ta kogin jodan aka kafa musu sharudda na shekarun wadanda za su je sallar.

Gwamnatin yahudawan ta bayyana dalilin hakan da cewa yana da alaka ne da batun tsaro kai tsaye, musamamn ma bayan harba wani makamin roka daga yankin Gaza zuwa cikin arewacin palastibnu da Isra’ila ta mamaye a cikin makonni biyu da suka gabata.

A kowane lokacin haratacciyar kasar Isra’ila kan fake da wasu dalilai domin muzgunawa al’ummar palastinu, tare da cin zarafinsu da kuma hana s gudanar wasu daga cikin muhimman lamurra na ibada da sunan harkar tsaro.

Tun a cikin shekara ta 2007 ce dai Isra’ila ta killace yankin zirin Gaza baki daya, tare da hana shigar da komai a yankin, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin wani mawucin hali, a lokaci guda talauci yana karuwa  atsakaninsu.

3318463

Abubuwan Da Ya Shafa: palestine
captcha