Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar hada mazhabaobin muslunci ta duniya, inda ya tir da abin da ya faru na harin ta’addanci kan masallacin Imam Sadiq (AS) a kasar Kuwait a ranar jiya a lokacin salla.
Bayanin ya ci gaba da cewa hari kan masallacin Imam sadiq (AS) a kasar Kuwait aiki ne ta’addanci da ya cancanci yin Allawadai da kakkausar suka daga dukaknin bangarori na duniya tare da yin kira da a dauki dkkanin madakan da suka dace wajen yin birki kan maganganu na tuzuru jama’a da rabawa kawunansu.
Kungiyar yan ta’addan nan masu da’awar kafa daular muslunci ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai harin kunar bakin wake yau a cikin Masallacin Imam Sadiq (AS) na mabiya Mazhabar Shi'a a kasar Kuwait, a lokacin da ake sallar Juma'a, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla ashirin da biyar tare da jikkatar wasu da dama.
A cikin wani bayani da kungiyar ‘yan ta’addan ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa ita ce ta shirya kai harin a cikin wannan masalaci, da nufin kashe wadanda ta kira kafurai, ta kun jinjina wa mutumin da ya kai harin, wanda ta bayyana shi a matsayin mai jihadi a tafarkin Allah kuma wanda ya yi.
Ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Kuwait ta sanar da cewa dan ta’addan da ya kai wanann hari dan kasar saudiyya ne kuma ya tarwatsa kansa ne da bama-bamai a lokacin da ake sallar Juma’a, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar masallata asirin da biyar yayin da wasu fiye da dari biyu suka samu munanan raunuka.
3319973