Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera Net cewa, gwamnatin ta sanmar da hakan biyo bayan harin ta’addanci da aka kai jiya a garin Sousse wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 39 tare da jikkatar wasu.
Habin Said firayi ministan kasar ta Tunisia ne ya sanar da hakana cikin wata sanarwa da ya karanta a jiya, inda ya ce sun yanke shawarar rufe masallatai 80 a fadin kasar domin fuskantar masu yada akidar ta’addanci.
Gwamnatin Tunisia ta sanar da cewa za ta rufe masallatan ne fiye da tamanin a fadin kasar na masu akidar kafirta musulmi wadanda ta ce a nan ne ake yada akidar ta'addanci da sunan addinin musulunci a kasar, tare da wanke kwakwalen samari da kuma tunzura su suna shiga kungiyoyin 'yan ta'adda da sauransu da sunan yakia tafarkin ubangiji.
Tun kafin wanann lokacin dai kasar ta Tunisia tana fuksnatr matsaloli tun bayan kawar da gwamnatin mutanen da ake kira masu kishin islama a kasar wadanda suke daukar nauyin yan ta’adda suna tura su zuwa kasashen ketare domin ta’addanci a hukumancein da ya bar mummuna tasirinsa a kasar ahalin yanzu.
A jiya ne aka kai hari a kasar inda aka kashe trawa yan kasashen ketare da kuma wasu daga cikin yan kasar ta Tunisia, bayan da wani dan ta’adda mai akidar kafirta musulmi ya kai hari kan wani otel, inda ya bude wuta ya yi ta kashe jama’a ba jib a gani, kafin daga bisani a shi ma a harbe shi.