IQNA

A Ranar 20 Ga Wannan Wata Na Ramadan Za A Fara Gasar Kur’ani Ta Kasar Algeria

22:34 - June 28, 2015
Lambar Labari: 3320695
Bangaren kasa da kasa, gasar karatu da harda da kuma tajwidin kur’ani mai tsarki karo na 12 a kasar Algeria za a fara ta a ranar 20 ga wannan wata na Ramadan mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na fananews.com cewa a ranar 20 zuwa 26 ga wannan wata na Ramadan mai alfarma gasar karatu da harda da kuma tajwidin kur’ani mai tsarki karo na 12 a kasar Algeria za a fara gudana a birnin Aljiers.

Mai’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar da cewa ta aike da goron gayyata zuwa ga kasashe 66 domin halartar wannan gasa, da suka hada har da kasashen da ba na musulmi ba, kamar Rasha, Canada, India da kuma Phlipines, domin musulmin kasar su samu halartar gasar duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye.

Muhamamd Khakpour mahardacin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran shi ne zai wakilci kasar a wannan gasa, wanda ya kai har zuwa mataki na biyu na tantacewa domin samun damar zuwa gasar.

An haifi Muhammad Khakpour a birnin mashahad kuma ya taka gagarumar rawa  abangarori na karatu da hardar kur’ani mai tsarki, a cikin shekara ta 1392 hijira shamsiyyah ya samu halartar gadar kur’ani ta kasar Jordan.

Maia;katar kula da harkokin addini ta kasar saudiyya ta sanar da cewa Muhammad Bin Ali Al-sudais yana daga cikin alkalan da za su yi alkalanci a wannan gasa, wanda kuma malami a bangaren koyar ilmomin kur’ani mai tsarki a jami’ar Madina.

3320109

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha