IQNA

Wadanda Suke Kambama Bakar Fuskar Amurka Suna Yin Ha’inci Ne Ga Alummar Kasa

22:38 - June 28, 2015
Lambar Labari: 3320697
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a lokacin da yake ganawa da iyalan wadanda suka yi shada ya bayyana cewa wadanda suke ta kokarin kambama Amurka da kuma bakar fuskarta su san cewa suna hainci ne ga al’ummmar kasa.


Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin Asabar ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da iyalan shahidan ranar 7 ga watan Tir da kuma wasu iyalan shahidan lardin Tehran don tunawa da zagayowar ranar da aka kai hari wa jami'an ma'aikatar shari'a ta Iran da yayi sanadiyyar wasu manyan jami'an kasar Iran ciki kuwa har da alkalin alkalai na lokacin Ayatullah Shahid Beheshti.

A jawabin da ya gabatar a wajen ganawar, Jagoran ya bayyana cewa kasar Iran da kuma al'ummarta suna da wani nauyi a wuyansu dangane da shahidai da kuma iyalansu, haka nan kuma yayin da yake ishara da sakon mai faranta rai da ke cikin irin tsayin dakan da shahidan suka yi a lokuta mabambanta, Jagoran cewa yayi: A yau kasar Iran tana bukatar tsayin daka, fahimtar makiya da kuma shirin tinkarar makiya a dukkanin fagage ciki kuwa har da fagen al'adu, siyasa da zamantakewa ta al'umma. A saboda haka wadanda suke kokarin rufe bakar fuskar makiya, lalle suna yin abin da ya saba wa manufa da kuma maslahar al'umma ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar daya daga cikin albarkokin juyin juya halin Musulunci na kasar Iran shi ne sake rayar da koyarwar Musulunci da kuma tabbatar da su cikin rayuwar al'umma. Daga nan sai ya ce: Daya daga cikin irin wadannan koyarwar, shi ne koyarwar da ke da alaka da shahada wanda aka tabbatar da ita a cikin al'ummarmu, ta yadda cikin kumaji da karfin gwiwa shahidan suke shiga fage. Ladar wannan kokari na su kuwa shi ne wannan babbar lada ta shahada, inda suka tafi wajen Ubangijinsu ba tare da wata matsala. Lalle ana iya ganin sakamakon wanann shahadar kuwa a cikin al'umma.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya bayyana samar da yanayi na jin daukaka a cikin iyalan shahidan da kuma samar da ruhi na tsayin daka a tsakanin al'umma a matsayin daya daga cikin albarkokin shahidai a cikin al'umma din. Sannan kuma yayin da yake ishara da harin da aka kai ranar 7 ga watan Tir shekara ta 1360 (hijira Shamsiyya) da yayi sanadiyyar shahadar Ayatullah Beheshti da wasu abokan aikinsa su 72, Jagoran cewa yayi: Manyan lamurra irin su harin 7 ga watan Tir da yayi sanadiyyar shahadar Ayatullah da wasu ministoci da ‘yan majalisa da wasu ‘yan siyasa da ma'abota juyi, wasu abubuwa ne da a dabi'ance suna iya dunkufar da wannan juyin na Musulunci. To amma albarkacin jinin wadannan shahidan, sabanin da abin da ake zato ne ya faru. Don kuwa bayan wannan harin sai kawukan al'ummar nan suka hadu waje, sannan kuma juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da tafiya a bisa sahihiyar hanyarsa.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa daya daga cikin albarkokin jinin shahidan ranar 7 ga watan Tir din shi ne tona asirin masu aikata wannan danyen aikin, Jagoran cewa yayi: Bayan wannan hari na 7 ga watan Tir, asalin fuskar wadanda suka aikata wannan danyen aikin kai tsaye, wadanda kuma shekara da shekaru kenan suke boye hakikaninsu, ta fito fili ga al'umma da kuma matasan kasar nan. Tsawon lokaci wadannan ‘yan ta'addan suka dauka suna tare da Saddam wajen yakar al'ummar Iran da kuma na Irakin.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana bayyanar hakikanin mutanen da suka buya ta bayan fage a ciki da wajen kasar Iran haka nan da wadanda suka yi shiru da kuma nuna jin dadinsu da abin da ya faru, a matsayin daya daga cikin albarkokin jinin shahidan wannan harin, inda ya ce: Bayan harin 7 ga watan Tir, marigayi Imam Khumaini, Allah Yayi masa rahama, yayi amfani da hakan wajen ceto wannan juyin juya hali na Musulunci daga kokarin da wasu suka yi na kawar da shi daga tafarkinsa da kuma dawo da shi kan asalin tafarkinsa da kuma bayyanar wa al'umma da hakikin tafarkin juyin.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin karfin gwiwan da al'ummar Iran suka samu bayan wannan hari, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wannan lamarin ya bayyanar wa makiya irin karfi da matsayin da juyin juya halin Musuluncin nan yake da shi cikin zukatan al'umma, sannan kuma sun fahimci cewa lalle fada da wannan juyin ba zai haifar musu da da mai ido ba.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin yadda asiri da kuma hakikanin ma'abota girman duniya da suke ikirarin kare hakkokin bil'adama ya bayyana a idon duniya bayan wannan hari a matsayin wani bangare na albarkokin da ke cikin jinin shahidan wannan hari inda ya ce: Wadannan mutanen da suka aikata wannan danyen aikin, a halin yanzu suna nan suke gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci a kasashen Turai da Amurka. Suna ganawa da jami'an wadannan kasashen, kai hatta ma akan shirya musu tarurruka su zo suna lakca kan batun kare hakkokin bil'adama.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan a matsayin wata babbar alama ta munafunci da kuma tsagoron lalacewar masu da'awar kare hakkokin bil'adama na duniya. Daga nan sai ya ce: Akwai shahidai dubu 17 a kasar nan da aka kashe su ta hanyar kisan kai (na ta'addanci), mafi yawansu mutane ne na gari da suka hada da ‘yan kasuwa, manoma, ma'aikatan gwamnati, malaman jami'a, kai har ma da mata da kananan yara. Amma wadanda suka aikata wannan danyen aikin suna nan suna rayuwa cikin ‘yanci a kasashen da suke ikirarin kare hakkokin bil'adama.

Ayatullah Khamenei ya bayyana sanya ruhi da kuma karfin tsayin daka a cikin al'ummar Iran a matsayin daya daga cikin albarkokin jinin shahidan na daban, sannan kuma yayin da yake ishara da gagarumin taron jana'izar shahidai 270 da aka gudanar a birnin Tehran a kwanakin baya, Jagoran cewa yayi: Irin wannan gagarumin taro da kuma shirin ko ta kwana bugu da kari kan so da kauna da aka nuna wani lamari ne da ke a matsayin kishiyar lalaci da rashin kyakkyawan fata.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana rashin jin dadi da kuma takaicinsa dangane da gazawar da ake nunawa wajen bayyanar da hakikanin matsayin da shahidan suke da shi, inda yayi kira da a kara kaimi a wannan bangaren.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana fahimtar makiya a matsayin daya daga cikin bukatar da ake da ita a halin yanzu, kamar yadda kuma yayi jan kunne da kokarin da wasu suke yi na boye hakikanin bakar fuskar makiyan yana mai ishara da wasu ayyukan ta'addanci da Amurka da kuma kawayenta suka aikata kan al'ummar Iran.

"Harin da aka kai ranar 7 ga watan Tir 1360" da "ruwan bama-bamai masu guba a garin Sardasht a ranar 7 ga watan Tir 1366" da "Kisan gillan da aka yi wa Shahid Saduqi a ranar 11 ga watan Tir 1361" da kuma "Kakkabo jirgin fasinjan Iran a ranar 12 ga watan Tir 1367" a matsayin wasu daga cikin misalan ayyukan ta'addancin Amurka da ‘yan amshin shatanta da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da su inda ya ce: Wasu ma sun yi amanna da cewa ya kamata a sanya wa wadannan ranakun sunan "Makon hakkokin bil'adama samfurin Amurka".

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne al'ummar mu su kara kaimin fada da makirce makircen makiya a dukkanin fagage ciki kuwa har da fagen al'adu, siyasa da zamantakewa a hanyar fahimtar hakikanin makiya.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Shahidi Muhallati, wakilin jagora sannan kuma shugaban cibiyar shahidai da lamurran da suka shafi masu sadaukarwa ya gabatar da jawabinsa inda yayi karin haske kan ayyukan da cibiyar ta gudanar.

3320191

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha