IQNA

Za A Gudanar da Wata Gasar Kur’ani Mai Tsarki A Ta Kanan Yara A Ghana

23:12 - July 02, 2015
Lambar Labari: 3322413
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar karatun kr’ani mai tsarki mai taken Taj Al-rahmah da ta kebanci kananan yara akasar Ghana.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ghana Web cewa, gasar za ta gudana ne daga ranar yau kuma yara daga bakin shekaru 9 zuwa 13 za su halarci gasar domin karawa da juna.

Yara 60 daga cibiyoyin addini guda 20 suka halraci wurin, kuma suke cikin shiri karawa da juna a bangarorin da za a gudanar da gasar, kuma 8 daga cikinsu ne kawai za su isa mataki na karshe.

Wadannan yara guda 8 za su yi karatu a gaban alakalai na gasar wadanda za su fiytar da dkkanin matakai na daya da na biyu da kuma na uku a tsakanin wadanda suka kara daga karshe.

An sanya wannan gasa ta zama a cikin watan Ramadan e domin kara karfafa gwiwar yara da matasa kan lamurra da suka danganci kur’ani mai tsarki a tsakanin mabiya addinin muslunci na kasar.

Wannan dais hi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan gasa  ajere da ta shafi kanan yara musulmi a kasar.

3322053

Abubuwan Da Ya Shafa: ghana
captcha