Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-qabs cewa, Ya’aqb Sanei ministan shari’a na kasar Kuwait ya bayyana cewa, bisa umarnin sarkin kasar Sheikh Jaber Ahmad Al-Jaber Al-Sabah a yau an gudanar da sallar Juma'a ta bai daya tsakanin 'yan sunni da kuma 'yan shi'a a babban masallacin kasar, tare da halartar sarkin da dukkanin mukarrabansa, domin tabbatar wa duniya irin hadin kai da ke akwai a tsakanin al'ummar kasarsa.
Ya ce dukkanin hudubobin sallar Juma’a na wannan mako an gudanar da su bisa batun hadin kai a tsakanin al’ummar kasar baki daya, tare da tabbatar way an ta’adda cewa ba za su iya kawo rarraba atsakanin al’umma ba.
Dangane da yadda aka gudanar da janazar shahidan masallacin Imam Sadeq (AS) kuwa, ya bayyana cewa hakan ya isa da sako ga dukaknin al’ummomin duniya cewa, jama’ar Kwait al’umma guda ce, wadda wani ba zai iya raba su ba.
3322457