IQNA

‘Yan Shi’a Da ‘Yan Sunna Sun Gudanar Da Sallar Hadin kai A Bahrain

23:33 - July 04, 2015
Lambar Labari: 3323168
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin shi’a da yan sunna sun gudanar da wata salla ta hadin kai tsakaninsu a babban masallacin shi’a na kasar.


Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, dubban mabiya tafarkin shi’a da yan sunna sun gudanar da wata salla ta hadin kai tsakaninsu a babban masallacin shi’a na kasar ta Bahrain, domin tabbatar da hadin kai.

Wannan mataki dai ya zo domin kalu balantar matakin da yan ta’adda suke barazanar dauka na kaddamar da hare-hare kan masallatan mabiya tafarkin shi’a a kasar ta Bahrain kamar yadda suka  yi a cikin wasu masallatai a wasu kasashen na larabawa a wannan mako, kuma a mako mai zuwa za a gudanar da wannan sal,aa wani masallaci na sunna.

Bayanin ya ci gaba da cewa masu tsatsauran ra’ayin salafiyanci da akuma akidar na ta kafirta musulmi su ne a kan gaba wajen yada irin wannan ra’ayi na ta’addanci a cikin kasashen larabawa da kuma duniiya baki daya.

Wasu daga cikin bangarorin Saudiyyah ne dai suke daukar nauyin yada irin wannan mummunar akida, wadda gwamnatin kasar ta doru a kanta, kuma take daukar nayin yan ta’adda domin aiwatar da manufarsu da suna  addini kuima bisa wannan akida ta su mai matukar hadari.

3322676

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha