IQNA

Babban Masallacin Nairobi Wurin taruwar Musulmin Kenya A Cikin Watan Ramadan

22:57 - July 05, 2015
Lambar Labari: 3323721
Bangaren kasa da kasa, dubban mabiya addinin muslunci a kasar Kenya suna taruwa a cikin babban masallacin birnin Nairobi fadar mulkin kasar domin gudanar da ayyukan ibada.


Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, idan mutane suna bayar da taimako ga wadanda ba su da shi suna kai wa a cikin masallaci domin raba wag are su.

Musulmi a kasar Kenya suna taruwa a cikin babban masallacin a kowace shekara a birnin Nairobi fadar mulkin kasar domin gudanar da ayyukan ibada da kuma yin taimako ga marassa galihu.

Saleh Mungaka daya ne daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar ta Kenya, wanda yake bayar da taimako na abinci ga marassa galihu a kowace shekara a cikin wannan wata mai alfarma, inda yakan mika shi zuwa ga masallatai.

Mungaka ya ce baya son wani musulmi ya kai azumi bas hi da abin da zai ci, kamar yadda kuma baya sona  samu wani musulmi ya rasa a bin da zai sahur da shi saboda rashi da talauci, a kan hakan yana bayar da taimako n abin gwargwadon iko ga musulmia  wannan wata mai alfarma.

A lokacin da yake bayyana hakan, ana cika manyan motoci na daukar kaya da abinci zwa babban masallacin birnin domin rarrabawa ga mabukata, wanda hakan ya sanya ya zama a bin koyi ga dukkanin sauran msuulmi da suke burin samun lada a wannan wata.

Musulmin Kenya kimanin kasha 30% cikin dari ne daga dukkanin al’ummar kasar miliyan 43, tn kimanin shekaru 1000 da suka gabata ne musulminci ya isa kasar ta hanayar yan kasuwa daga Oman.

3323510

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha