IQNA

Babu Dalilin Da Zai Sanya Bunkasar Ilimi Ta Ragu / Siyasa Tana Tafiya Da Bunkasar Ilimi

22:59 - July 05, 2015
Lambar Labari: 3323722
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan malamai, masu bincike da sauran jami'an jami'oin kasar Iran inda ya bayyana irin rawar da malamai za su iya takawa wajen koyarwa da kuma tarbiyyar al'umma ma'abociyar kokari da imani da ci gaba a matsayin wata rawa maras tamka don haka ya kirayi malaman da su nesanci shiga cikin wasu batutuwa na bayan fage.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yayin wannan ganawar wacce ta dauki sama da awanni biyu ana yenta, bayan ya saurari mahanga da kuma shawarwarin wani adadi na malaman jami'an, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin tasirin da malamai suke da shi cikin zukatan daliban jami'an a matsayin wata dama maras tamka daga nan sai ya ce: Ku yi amfani da wannan dama mai girma wajen tarbiyyantar da matasa ma'abota "riko da addini, masu kishin kasa, masu kokari da kumaji, masu riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, masu kyawawan halaye, jarumai, masu dogaro da kansu da kuma kyayyakwar fata ga makomarsu". Haka nan kuma ku tarbiyyantar da mutanen da za su taimaka wajen ciyar da kasar nan gaba.

Jagoran ya bayyana wadatuwa daga ‘yan kasashen, kyakkyawar fahimtar yanayin da kasa take ciki da kuma makomarta, haka nan da kuma nuna damuwa kan kokarin kawo karshen ‘yanci na kasa da ake da shi, a matsayin wasu siffofi da wajibi ne matasa su zamanto suna da su, daga nan sai ya ce: Yana da kyau malamai masu girma su samar da irin wadannan matasan ta hanyoyi da kuma tsari irin nasu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana malaman jami'an a matsayin kwamandojin yakin lalata al'adu da makiya suke yi, don haka sai ya ce musu: Tamkar kwamandojin kallafaffen yaki na shekaru 8, ku yi kokari wajen jagorantar wadannan jami'an yakin lalata al'adu wato wadannan matasa daliban jami'a, wanda shi kansa wannan fagen, wani fage ne na yaki.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana jin dadi da farin cikinsa kan kasantuwar sama da masu bincike kan harkokin ilimi dubu 70 a jami'oin kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Mafi yawan gaske na wadannan malaman, mutane ne muminai, masu riko da addini da kuma koyarwar juyin juya halin Musulunci, wanda hakan lamari ne mai matukar muhimmancin gaske. Abin alfahari ne ga kasar nan.

Ayatullah Kahmenei ya kirayi jami'an ma'aikatun "ilimi, bincike da fasaha" da "lafiya" zuwa ga girmama irin matsayin da wadannan malamai muminai ma'abota juyin juya hali suke da shi yana mai cewa: Mutanen da ba su damuwa da irin wannan farfaganda mai cutarwa da ake yi a kansu, sannan suka ci gaba da ayyukansu masu muhimmanci, lalle wajibi ne a kula da kuma jinjina musu.

Jagoran ya bayyana nasarar da Iran ta samu na hawa mataki na 16 a fagen ilimi na duniya a matsayin sakamako na kokari ba kama hannun yaro da jami'oi da cibiyoyin ilimi na Iran suka yi tsawon shekaru 10 zuwa 15 din da suka gabata ne. Daga nan sai ya ce: A halin yanzu dai an sami raguwar irin gagarumin ci gaba na ilimi da Iran ta samu. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati su kara himma wajen ganin ba a sami koma bayan ci gaban ilimi ba. Su yi kokari wajen ganin an samu ci gaban da ake bukata daidai da bukatar da ake da ita a kasar nan.

Har ila yau yayin da yake magana kan abubuwan da suke rage irin ci gaban da ake samu a kasar Iran a fagen ci gaban ilimi, Jagoran yayi kakkausar suka kan yadda ake shigo da wasu batutuwa na bayan fage da kuma lamurran da suka shafi siyasa fagen ilimi. Daga nan sai ya ce: Na'am wajibi ne fagen jami'a ya zamanto wani fage ne na fahimta ta siyasa da kuma ilimi na siyasa, to amma siyasantar da fagen ilimi da kuma komawa ga abubuwa na bayan fage lamari ne da ke cutar da ci gaban ilimi, gagarumar cutarwa.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin rawar da malamai da jami'ai masu gudanar da cibiyoyin ilimi na kasar Iran za su taka wajen fada da makirce-makircen makiya inda ya ce: Manufar makiya wajen sanya wa Iran takunkumi, ba ta da alaka da batun nukiliya ko batun take hakkokin bil'adama ko ta'addanci ba, don kuwa su din nan su ne tushe da kuma cibiyar tarbiyyartarwa da kuma yada ta'addanci da kuma take hakkokin bil'adama. Face dai manufarsu ita ce hana Iran kai wa ga matsayin da ya dace da al'ummar a fagen ci gaba. A saboda haka wajibi ne, ta hanyar fahimtar irin matsayin da ake da shi, a ci gaba da wannan yunkuri na ciyar da kasar nan gaba, wanda rawar da malaman jami'a da sauran ma'abota ilimi da bincike za su taka a wannan fagen, wata gagarumar rawa ce.

Tun da fari dai sai da wani adadi na malaman jami'a da masanan suka gabatar da jawabansu inda suka yi ishara da mahangarsu kan yadda za a ciyar da kasar Iran gaba a fagen ilimi da kuma irin matsalolin da ake fuskanta bugu da kari kan hanyoyin da suke ganin za a iya magance su.

3323157

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha