IQNA

17:46 - July 06, 2015
Lambar Labari: 3324170
Bangaren kasa da kasa, a yau za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki karo na goma sha biyu tare da halaratr wakilin Iran a birnin Algiers.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na radioalgerie.dz cewa, gasar za a fara ta ne tare da halaratr shugaban kasar Abdulaziz Butaflika.

Muhammad Isa ministan mai’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar da cewa ta aike da goron gayyata zuwa ga kasashe da dama domin halartar wannan gasa, da suka hada har da kasashen da ba na musulmi ba, domin musulmin kasar su samu halartar gasar duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye, ya ce ya zuwa yanzu kimanin kasashe 49 ne suka amsa cewa za su halarci gasar.

Ya ci gaba da cewa wannan bababr dama ga musulmin kasar da su mayar da hankali ga lamrrun kur’ani mai tsarki, musamman ma ganin cewa suna daga cikin wadanda aka sani ta fskar karatun kur’ani da kuma hararsa a nahiyar, akan za a ci gaba da mayar da hankali ga wannan gasa.

Dangane da tarisin kuwa ya bayyana cewa, ko shakka babu gudanar da irin wannan gasa a kasarsa tana da matukar muhimamci, musamamn ma idan aka yi la’akari da yanayin da matasa suke ciki a yanzu, suna da bukatuwa matuka zuwa ga wani abu da zai rika tunatarsu addininsu da kuma koyar littafinsu mai tsarki.

Ma’akatar kula da harkokin addini ta Iran ta ce Muhamamd Khakpour mahardacin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran shi ne zai wakilci kasar a wannan gasa, wanda ya kai har zuwa mataki na biyu na tantacewa domin samun damar zuwa gasar.

Wanda kuma ya taka gagarumar rawa a bangarori na karatu da hardar kur’ani mai tsarki, a cikin shekaru biyu da suka gabata ya samu halartar gadar kur’ani ta kasa da kasa, hakan nan kuma  wannankaro zai wakilci kasarsa a Algeriya.

3323793

Abubuwan Da Ya Shafa: Algeria
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: