Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, an gudanar da wannan gasa ne tare da himmar babbar cibiyar kula da harkokin kur’ani da hardarsa da kuma sauran harkokin addinin muslunc ta kasar.
Mahardata da makaranta 57 ne daga sasasn kasar suka halarci wannan gasa, inda suka kara da juna a bangaroron harda da kuma karatun kur’ani da kuma hadisi gami da kalmomin kur’ani mai tsarki.
Sheikh Muhammad Bashir Jibril shi ne shugaban cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar, kamar yadda kuma shekh Abdullah Abdullatif shi ne wakilin kasar a gasar kur’ani ta duniya, ya bayyana cewa wannan gasa tana da matukar muhimmanci ga matasan kasar musamamn ma masu mayar da hankali kan lamarin kur’ani.
Ya ci gaba da cewa an kammala wannan gasa lami lafiya ba tare da samun wata matsala ba, kuma suna fatan wannan ya zama wata masomiya ta ci gaba da gudanar da irin wannan aiki na alkhairia kowace shekara.
Dag cikin wadanda suka halarta kuma, sun bayyana matukarfarincikinsu dangane da yadda gasar ta gudana a cikin tsari, tare da yin fatar gain hakan ya dore a nan gaba.
3325502