IQNA

Muslmin Kasar Amurka Za Su sake Gina Wa Bakaken Fata Majami’oinsu Da Aka Kone

23:42 - July 10, 2015
Lambar Labari: 3326312
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Amurka sun fara gudanar da gangami na hada kudade domin sake gina majami’oin mabiya addinin kirista bakken fata da aka kone musu.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Zayid Shaker daya daga cikin jagororin maiya addinin muslunci a kasar ta Amurka ya bayyana cewa, yanzu haka musulmi a kasar ta Amurka sun fara gudanar da gangami na hada kudade domin sake gina majami’oin mabiya addinin kirista n na kasar mallakin bakken fata da aka kona da wuta.

Ya ci gaba da cewa akwai majamiu guda 7 da aka kona dukkaninsu na mabiya addinin kirista bakaken fata ne, kuma za su gyara su domin nuna raham da jin kai irin na addinin muslunci ga dukkanin ‘yan adam.

A cikin yan lokutan da suka gabata an kai hare-hare a majamiu na mabiya addinin kirista a sassa daban-daban na Amurka musamamn a Chalston, inda aka kona tare da kasha adadi mai yawa na bakaen fata a cikin majamiu.

Musulmin sun bayyana cewa za su yi hakan domin kara tabbatar wa Amurkawa cewa addinin sun a zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da saurana addinai, da kuma jin kai ga dukkanin bil adama, wanda kuma hakan shi ne hakikanin koyarwa ta addinin muslunci.

A mahangar addinin muslunci babu wani banbanci tsakanin mutane ko fararare ne ko bakake, dukkaninsu ‘yan adam ne bayin Allah madaukakin sarki.

3326129

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha