IQNA

Wasu Malaman Jami’oin Birtaniya Ba Su Amince Da Dokar Yaki Da Ta’addanci A Kasar Ba

23:27 - July 12, 2015
Lambar Labari: 3327268
Bangaren kasa da kasa, daruruwan malaman jami’a a kasar Birtaniya sun nuna rashin amincewarsu da dokar da aka kafa a kasar ta yaki da ta’addanci tare da bayyana hakan da cewa zai cutar da musulmi ne kawai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, a jiya daruruwan malaman jami’a a kasar Birtaniya sun nuna rashin amincewarsu da dokar da aka kafa a kasar ta yaki da ta’addanci tare da bayyana hakan da cewa zai takura ma mabiya addinin muslunci ne akawar.

Bayanin wanda malaman jami’a 280 suka saka ma hannu, ya nuna rashin amincewa da dokar, domin kuwa za ta takura ma musulmi alhali akasarin mabiya addinin muslunci ba yarda da ta’addanci ba, kuma hakan ba shi da alaka da abin da muslmi sukia yi Imani da shi.

Gawmnatin kasar Birtaniya ta kafa wannan doka da nufin fuskantar ayyukan ta’addanci da kma masu yada tsauran ra’ayi kasar da ke mtasa zuwa ga shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda, da ke tafiya wasu kasashe domin kai hare-hare.

Da dama daga cikin muuslmin kasar ta birtaniya sun yi kira ga mahukuntan kasar da su sake yin nazari kana bin da yake faruwa, tare da daukar matakan da suka dace domin fuskantar wannan lamari, domin kuwa suna ganin akwai sakaci daga bangaren mahukunta.

Wannan doka za ta bayar da dama a bincika mutane da kuma shige da ficensu a kasar da kuma cikin gida, wanda ake ganin zai takura ma mtane matuka.

3327052

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha