Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakjalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iina cewa, wasu daga cikin mabiya addinin muslunci a kasa Birtaniya sun fara da wani kamfe na yaki da tsatsauran ra’ayi a tasakanin musulmin da suke zaune a kasar domin dora su kan sahihin tafarki na addini.
Sulaiman Najdi daya daga cikin wadanda suka shirya wannan kamfe ya bayyana cewa, bababr manufarsu ita ce wayar da kan mabiya addinin muslunci a ba su da masaniya kann addini, wadanda kuma su ne suka fi sauran yaudaruwa zuwa shiga kungiyoyin ta’addanci da suna jihadi.
Ya ci gaba da cewa babban misalign hakan shi ne yadda matasa suke shiga cikin kungiyoyin da suke bullowa a yanzu da suka hada da yan ta’adda a cikin kasashen larabawa da suke kashe musulmi da wadanda ba musulmi ba da sunan yaki a tafarkin ubangiji.
Sanannen lamarai dai cewa kasar Birtaniya na daga cikin kasashen turai da suke faa da matsalar shiga kungiyoyin yan ta’adda da matasan kasar suke yi, inda suke yin tafiya domin hadewa da wadannan kungiyoyin a wasu as ashen ketare.
Bayanan baya-bayan nan dai sun tabbatar da cewa akwai yan kasar ta birtaniya wadanda addainsu ya kai daruuwa a ketare suna yaki tare da kungiyoyin ‘yan ta’adda, wanda kuma wayar da kan irin wadannan matasa ne ya sa aka bullo da wannan kamfe.
3327429