Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin Talata ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Iran da ‘yan majalisar ministocinsa inda yayin da yake karin haske kan wasu bangarori na wasikar da Amirul Muminin Ali (a.s) ya aike wa Malik al-Ashtar (gwamnan da ya aike Masar) ya bayyana cewar: Garkuwa da kariya ta ruhi da zuciya da kuma tunani, su ne babban maganin dukkanin matsaloli. Tabbas tunani cikin (littafin) Nahjul Balaga na Shugaban masu tsoron Allah, yana samar da irin wannan kariya da garkuwa da ake bukata.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin da shugaban kasar na Iran yayi a farko-farkon ganawar dangane da sakamakon tattaunawar nukiliya (da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nuna godiya da kuma jinjinawarsa ga tawagar Iran a wajen tattaunawar saboda irin kokari ba kama hannun yaro da suka yi tsawon wannan lokacin.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da girman matsayin da Malik al-Ashtar ya ke da shi wajen Amirul Muminin (a.s), Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Wasikar Imam Ali bn Abi Talib, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ga irin wannan mutum mai girman matsayi wani lamari ne abin dubi da tuntuni cikinsa.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan ayyuka da nauyin da ke wuyan jami'an gwamnati cikin wannan wasika ta Amirul Mumini (a.s) ga Malik Ashtar inda ya ce: "karbar haraji da sauran hakkokin da gwamnati take da su a wuyan al'umma", kare lafiyar mutane da kasarsu, kwadaitar da mutane zuwa ga gaskiya da kyautatawa, sannan da kuma gina kasa, wadannan su ne ayyuka na asali da Amirul Muminin (a.s) a cikin wannan wasika tasa ya bayyana su a matsayin nauyin da ke wuyan shugabanni.
Ayatullah Khamenei ya bayyana: "kiran shugabannin musulmi zuwa ga tsoron Allah a duk yanayi da halin da suke ciki", "Ba da dukkanin himma wajen aiwatar da farillai da sunnoni da mustahabbai", "Sanya Allah Madaukakin Sarki cikin zuciya da harshe da kuma aiki" da kuma "yin watsi da son zuciya da sha'awace-sha'awace" a matsayin wasu umurni masu muhimmancin gaske da Amirul Muminin (a.s) yayi wa Malik wasicci da su a matsayin abubuwan da za su taimaka masa wajen gina kai da tsarkake zuciyarsa.
Yin hukunci na adalci a kan jami'an da suka gabata yana daga cikin abubuwan da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada kansu yana mai tabbatar da hakan cikin wannan wasika da umurni na aiki da Imam Ali (a.s) ya aike wa Malik Ashtar.
Ayatullah Khamenei ya bayyana aiki na kwarai a matsayin mafi kyawun guzurin shugaba a lokacin shugabancinsa inda ya ce: Ba za a yi kuskure cikin hukuncin da aka yanke bayan tunani mai zurfi da bincike na kwarai ba. A saboda daga irin wannan hukunci na mutane za a iya fahimtar shin mutum jami'in gwamnati na kwarai ne ko kuma a'a.
"Kiyaye zuciya daga fadawa ramin bata" da kuma "gabatar da takalifi na Ubangiji sama da dukkan komai" wasu wasicci guda biyu ne na daban da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da su a yayin da yake ci gaba da karanto wani bangare na wannan wasika ta Amirul Muminin (a.s) ga Malik Al-Ashtar inda daga nan sai ya ce: Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya kasance babbar alamar aiki da wadannan wasicci na Ubangiji.
Ayatullah Kahemeni ya bayyana "kaunar mutane daga tsakar zuci" da kuma "so da rufe ido kan ayyukan mutane" a matsayin wasu daga cikin umurnin Imam Ali (a.s) ga Malik Al-Ashtar cikin wannan wasika tasa, daga nan sai ya ce: Bisa umurnin Amirul Muminin, wajibi ne a rufe ido da ku da kai daga kura-kuran mutane, koda yake ban da wajajen da aka take iyakokin Ubangiji ko kuma wajen da ya zamanto ana fada ne da Musulunci da kuma hukuma ta Musulunci.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan wasika ta Imam Ali bn Abi Talib (a.s) ga Malik Ashtar a matsayin wata ajiya da kuma guzuri mai kimar gaske ta al'adu da rayuwar al'umma. Daga nan sai kuma ya gode wa ‘yan majalisar ministocin saboda irin ayyuka da kokarin da suke yi inda yayi musu fatan alheri cikin ayyukansu.
Kafin jawabin Jgaoran juyin juya halin Musuluncin dai sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa.
A jawabin nasa, shugaba Ruhani yayi ishara da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyan kasar Iran inda ya bayyana tsananin godiyarsa ga irin shiryarwa da kuma goyon bayan da Jagoran yake ba wa gwamnatinsa da kuma tawagar masu tattaunawar, yana mai fatan hakan zai zamanto mafarin kawo karshen irin matsin lamba da kuma tuhumce-tuhumce maras tushe da makiya suke yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kana kuma wani sabon shafi na ci gaban kasar Iran.
A ci gaba da jawabin nasa, shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da gabatar da wani rahoto kan ayyukan da gwamnatin tasa ta yi.
Yayin da yake ishara da irin nasarori da kuma matsalolin da gwamnatin tasa take fuskanta tsawon shekaru biyun da suka gabata, shugaba Ruhani ya bayyana kokarin kulla kyakkyawar alaka da kasashen makwabta da kuma ci gaban tattaunawar nukiliya da ake yi a matsayin wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin tasa ta yi a fagen siyasar waje. Daga nan sai ya ce: A daidai lokacin da yankin nan yake fuskantar matsalolin rikice-rikice da ayyukan ta'addanci, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai goyon bayan kasashen yankin da suke fuskantar matsalar ta'addanci. Kuma ko shakka babu za ta ci gaba da hakan.
A fagen tattalin arziki, shugaban kasar na Iran yayi karin haske kan irin ayyukan da gwamnatin tasa ta yi a wannan fagen da suka hada da kara karfafa tattalin arzikin kasa, dakatar da rage yawan faduwar darajar kudi, rage yadda ake shigo da alkama, kara yawan kayayyakin da ake fitar da su waje.; daga nan sai ya ce: har ila yau kuma gwamnati tana da wasu tsare tsare na magance matsalar rashin aikin yi da ake fuskanta.
Daga karshe dai shugaba Ruhani ya sanar da aniyar gwamantinsa ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen magance matsalolin da ake fuskanta a kasar Iran.
3328203