Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iina cewa, kasashen Saudiyyah, Jibuti, Masar, Aljeriya, Qatar, Kuwait, Bahrain, Imarat, Turkiya, Lebanon , Jordan, Syria, Yemen, Libya, palastine, Sudan, Malayzia, Indonesia, Wakafin Sunna a Iraki, Thailand, Singapor, Ukraine, Rasha da kuma tsibirin Crimea duk sanar da yau sallah.
Tashar Sky News Arabic ta sanar da cewa, kwamiticon musulmi a kasashen Amurka, Australia, China da Japan, Korea ta kudu da Philipines, da kuma kasashen nahiyar turai gami da yankin Balkan, duk sun sanar da yaua matsayin ranar farko ta watan shawal da kuma salla.
Sai kuma wasu daga cikin kasashe kamar su Oman, Morocco, Burunei, Azarbaijan, Azbakistan, Ghana, Tajikistan, Afghanistan, Pakistan da kuma wakafin shi’a a na kasar Iraki, saboda rashin ganin wata ajiya, hakan ya sanya su cika azumin watan Ramadan, tare da sanar da gobe a matsayin salla.
Jamhuriyar muslunci ta Iran ma ta sanar da rashin ganin wata a jiya, a kan hakan gone ne salla a kasar.
3328873