Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na kasar Yemen Saba’anet cewa, Abdulmalik Badruddin Alhuthi jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya taya al’ummar musulmi na kasar da kuma rundunar sojin Yemen murnar barka da salla tare da yin kira da a kara zama cikin shirin fuskantar ta’addancin Saudiyya da yan koranta.
A cikin wani bayani da ya gabatar a yau wanda gidan talabijin na kasar ya watsa kai kai, ya bayyana cewa kasar ta shiga cikin wani yanayi da ke bukatar a yi amfani da dukaknin karfi domin mayar da martini kan ta’addan Saudiyya a kan al’ummar kasar.
Ayyukan kisan kisan kiyashin sa masarautar Saudiyya ke aiwatarwa kan fararen hular kasar Yemen ya zuwa yanzu dai yay i sanadiyyar mutuwar dubban faren hula da kuma jikaktar wasu dubban na daban, duk kuwa da cewa bangaroro na kasa da kasa sun kauda kansu akn abin da yake faruwa.
Y ace yana da tabbaacin cewa al’ummar kasar Yemen za ta yi nasara ayakin da take yin a kre kai daga ta’addancin Saudiyya, hakan nan kuma a halin yanzu abin da yake faruwa na kara samun hadin kai tsakanin al’umma wani abu ne mai matukar muhimmanci
Yanzu haka dai ana ci gaba da fatatwa tsakanin sojojin kasar da mayakan Huthi ke marawa baya da kuma mayakan alkaida masu samun goyon bayan saudiyya, wanda suke mara baya ga Hadi Mansur.
3328938