IQNA

Domin Amincewa Da yarjejeniyar Nukiliya Dole A Bi Hanyoyi Na Doka / Kiyayen Tsaron Kasa

23:46 - July 19, 2015
Lambar Labari: 3330195
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya yi shara da matsayin yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa a kan shirin Iran da cewa ya zama wajibi a bi hanyoyui na doka, ko an amince ko ba a mince ba dai ladar wadanda suka tattaunawar tana nan Insha Allah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Asabar ce miliyoyin al’ummar musulmi na birnin Tehran, kamar sauran ‘yan’uwansu na sauran garuruwan Iran, suka gudanar da sallar idin karamar salla bayan kwanaki talatin na azumi a Musalla na Imam Khumaini (r.a) da ke birnin Tehran karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A lokacin da yake gabatar da hudubar farko ta sallar idin, Ayatullah Khamenei ya taya dukkanin al’ummar Iran da sauran al’ummomin duniya murnar wannan rana ta idi inda ya bayyana watan Ramalanan na bana a matsayin watan ruwan albarkoki na Ubangiji a kan al’ummar Iran, yana mai cewa: azumi a irin wadannan ranaku na tsananin zafin rana, tarurruka na tilawar Alkur’ani, tarurruka na addu’oi da kankan da kai a gaban Allah, gudanar da tarurruka na shan ruwa a masallatai da kan tituna sannan daga karshe kuma gudanar da gagarumin jerin gwanon Ranar Kudus ta duniya, dukkanin wadannan wasu alamomi ne na irin wadannan albarkoki na Ubangiji.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Ingantacciyar hanyar fahimtar al’ummar Iran ita ce dubi cikin irin wadannan abubuwan. Hakikanin da suke nuni da cewa haka al’ummar Iran suke a fagen ibada, haka nan a fagen fada da ma’abota girman kai ma haka suke da kuma nuna wa sauran al’ummomi ma.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da taken “Allah Ka La’anci Isra’ila” da “Allah Ka La’anci Amurka” da al’ummar Iran suka dinga rerawa a lokacin jerin gwanon Ranar Kudus ta Duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Ta hanyar irin wadannan matsaya da take ne ya kamata a fahimci wannan gagarumin yunkuri na al’ummar Iran, ba wai ta abubuwan da makiya masu mummunar aniya suke fadi ba, wanda abin bakin cikin shi ne cewa hatta a cikin gida a kan sami wasu mutane da suke fadin irin wadannan maganganu (na makiya).

A huduba ta biyu kuwa, yayin da yake ishara da abubuwa masu bakanta rai da suke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne cewa wadansu hannaye marasa albarka sun cutar da wasu al’ummomi masu yawa na wannan yankin a kasashen Yemen, Bahrain, Palastinu da Siriya, wanda hakan wani lamari ne mai muhimmancin gaske ga al’ummar Iran.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki lokaci mai tsawo na huduba ta biyun wajen karin haske kan batun yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Batu na farko da Jagoran ya tabo a wannan bangaren shi ne mika godiyarsa da jami’an da suka dau nauyin gudanar da wannan tattaunawar mai tsawo da sarkakiyar gaske saboda irin kokari da aiki ba kama hannun yaron da suka yi inda ya ce: Wajibi ne abi hanyoyi na doka wajen tabbatar da matanin da aka shirya na yarjejejeniyar, to amma dai ko an amince da shi ko ba a amince ba, lalle ladar aikin masu tattaunawar nan tana nan a wajen Allah insha Allah.

Ayatullah Khamenei ya kirayi jami’ai masu gudanar da bincike kan matanin yarjejeniyar da aka shirya da cewa: Ku gudanar da ayyukan da kyau da kuma sanya ido sosai kuna masu la’akari da maslaha da amfanin kasa don ku gabatar wa al’umma da wani karbabben abu.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan wajibcin fada da duk wani kokari na mummunan amfani da matanin da aka tsara na yarjejeniya da makiyan Iran za su yi, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Ko an amince da matanin da aka tsara din ko ba a amince da shi ba, ba za mu taba bari wani yayi Karen tsaye ga tushen tsarin Musulunci na Iran ba.

Har ila yau kuma, yayin da yake magana kan maganganu da barazanar da wasu suke yi wa Iran da kuma kokarin da makiyan suke yi wajen cutar da tsarin kariya na Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Da yardar Allah za a kiyaye irin karfin kariya da Iran take da shi da kuma hurumin tsaron kasar Iran. Sannan kuma ko da wasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ga son wuce gona da iri da tinkaho da karfi na makiya ba.

Ci gaba da goyon bayan abokan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wannan yankin shi ne abu na gaba da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da shi a ci gaba da magana kan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma din.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ko an amince da matanin da aka tsara din ko ba a amince da shi ba, al’ummar Iran ba za ta taba daina goyon bayan al’ummomin Palastinu da ake zalunta, Yemen, Bahrain da al’umma da gwamnatocin kasashen Siriya da Iraki da mujahidan kasashen Labanon da Palastinu ba.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa ta kowace fuska siyasar al’umma da gwamnatin Musulunci ta Iran ba za ta taba sauyawa ba a fagen fada da gwamnatin Amurka ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Babu wata tattaunawa da za mu yi da Amurka kan batutuwan da suka shafi Gabas ta tsakiya, wannan yanki da kuma duniya ba, in dai ba cikin ‘yan wasu batutuwa na musamman ba kamar irin wannan na nukiliya wanda a baya ma mun taba yin hakan.

Har ila yau kuma yayin da yake tsananin sukar bakar siyasar Amurka ta goyon bayan gwamnatin ‘yan ta’adda mai kashe kananan yara ta Sahyoniyawa da kuma bayyana kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a matsayin kungiyar ta’addanci, Jagoran cewa yayi: akwai bambanci da sabanin kasa da sama tsakanin siyasarmu da siyasar Amurka a wannan yankin. A saboda haka ta yaya za mu iya tattaunawa da wadannan mutanen.

A ci gaba da jawabin nasa kan batun nukiliyan, Ayatullah Khamenei yayi ishara da maganganu baya-bayan nan da jami’an Amurka suke ta yi kan yarjejeniyar nukiliyan inda ya ce: Cikin ‘yan kwanakin nan jami’an a kokarinsu na magance matsalolinsu na cikin gida, jami’an Amurka suna ta maganganu, to amma babu gaskiya cikin abubuwan da suke fadin.

Yayin da yake magana kan daya daga cikin irin wadannan maganganu nasu, wato maganar da suke yi na cewa sun hana Iran kera makaman nukiliya, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Mu dai tun shekarun da suka gabata, bisa riko da koyarwar Musulunci, muka fitar da fatawar haramcin kera makaman nukiliya. Shari’a ta haramta mana kera makaman nukiliya. To amma Amurkawa duk kuwa da a wasu lokuta sukan yi magana kan muhimmancin wannan fatawar, amma duk da haka suna ci gaba da yada farfaganda ta karya da ikirarin cewa barazanarsu ce ta hana Iran kera makaman nukiliya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Jami’an gwamnatin Amurka na yanzu suna maganar cewa al’ummar Iran ta mika wuya, kafin wannan lokaci ma shugabannin Amurka guda biyar sun kasance masu wannan fata (na ganin Iran ta mika musu wuya), to amma ko dai sun mutu ko kuma sun bace cikin tarihi. Don haka kai ma kamar su, ba za ka taba ganin mika kan al’ummar Iran ba.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da ikirarin da shugaban Amurka yayi kan irin kura kuran da suka yi a baya kan Iran ciki kuwa har da goyon bayan juyin mulkin 28 ga watan Mordad da aka yi a Iran da goyon bayan Saddam Husain da suka yi da sauransu, Ayatullah ya bayyana cewar: Wadannan wasu bangare ‘yan kadan ne na irin wadannan kura-kuran, amma kawai wasu kura-kuran masu yawan gaske da har ya zuwa yanzu Amurka ba ta shirya ta amince da su ba.

Jagoran ya shawarci jami’an Amurkan da su kawo karshen irin wadannan kura-kurai da suke yi don kada jami’an kasar masu zuwa su ma su zamanto masu bayyana cewar sun yi kuskure.

Haka nan kuma yayin da yake sake jaddadawa kan tsayin dakan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Kimanin shekaru sha biyu kenan manyan kasashen duniya guda shida suke ta kokari wajen ganin sun dunkufar da fasahar nukiliya a Iran, kamar yadda wasu ma suke fadin cewa za su kawo karshen wannan shiri na nukiliya na Iran. Amma a halin yanzu an tilasta musu amincewa da ci gaban ayyukan dubban bututun tace sinadarin uranium a kasar Iran da kuma ci gaba da gudanar da bincike da ci gaban fasahar nukiliya a Iran. Hakan alama ce ta karfi da tsayin dakan Iran.

Jagoran ya bayyana irin karin ci gaba da karfin da Iran take yi a kullum a matsayin wata alama ta tsayin dakan al’ummar Iran da kuma kwarewar masanan kasar, don haka sai Jagoran ya jinjinawa shahidan da suka rasa rayukansu a tafarkin ciyar da fasahar nukiliyan din gaba da iyalansu.

A karshen hudubar tasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara ga maganar shugaban Amurka na cewa suna da karfin da za su ruguza sojojin Iran inda ya ce: Mu dai ba ma maraba da duk wani yaki sannan kuma ba za mu fara ba, to amma idan har hakan ta faru, to Amurka ce za ta debi kashinta a hannu.

3329071

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha