IQNA

23:50 - July 22, 2015
Lambar Labari: 3332263
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta fitar da wani bayani wanda acikinsa take bayyana harin da aka kai kasar Turkiya da cewa aiki na ta’addanci da bas hi da wata alaka da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na na oic-oci.org cewa, wannan kungiya ta fitar da wani bayani wanda a cikinsa take bayyana harin da aka kai a garin Suruch da ke kudancin kasar Turkiya da cewa aiki na ta’addanci da ba shi da wata alaka da yan damataka da kuma addini.
Bayanin ya ci gaba da cewa masu aikata irin wadanna ayyka suna kokarin danganta kansu da addinin muslunci ne da nufin bata masa suna a idon duniya, amma kuma ya zama wajibi sauran al’ummomi su san  cewa wadannan ayyuka ba su da wata  danganta da wani addini, balanta musulunci.
Kungiyar ta ce tana yin Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin na Turkiya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, haka nan kuma  tana yin kira da adauki dukkanin matakai na gudanar da bincike kan lamarin, domin gano masu hannu a ciki tare da gurfanar da su.
Ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Turkiya ta ce bisa ga binciken da aka gudanar an gane cewa an kai harin ne ta hanyar kunar bakin wake, kuma kungiyar IS ce take da alhakin kai wannan hari, bayanin ya ce tuni jami’an tsaro suka fara gudanar da bincke domin gano duk wadanda suke da alaka hakan domin kame su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

 

Sai dai a nasu bangaren da dama daga cikin jagororin Kurdawa na yankin sun dora alhakin wannan hari a kan gwamnatin Turkiya, inda suka ce ita ce babbar mai masaukin dukkanin taimako ga ‘yan ta’addan IS a hukumance, da suke fitowa daga kasashen duniya daban-daban, da suke shiga cikin kasashen makwabta  domin kai hare-hare, inda lamarin a halin yanzu kuma ya iso har cikin kasar ta Turkiya.

3331782

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: