Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, bayan killace birnin Falluja yan taaddan Daesh suna gudu ta hanyar yamacin Ramadi suna shiga cikin Syria, yayin da kuma wasu daga cikinsu suke shiga cikin Turkiya domin tsira da rayukansu.
Abdulrahman Nimrawi shugaban majalisar dokokin yankin na Fallujah ya bayyana cewa, wannan wani farmaki ne da sojojin kasar suka fara domin tabbatar da sun tsarkake yankin kafin fara babban farmaki na tsarkeke lardin baki daya.
Shi ma a nasa bangaren Faleh Al-isawi mataimakin shugaban majlaisar dokokin lardin Anbar ya tabbatar da labarin tserewar manyan kwamandojin yan ta’addan daga yankinsuna shiga makwabta.
Jaridar Zaman Emroz ta bayar da rahoto tun ranar 12 ga watan Yunin da ya gabata kan cewa, ‘yan ta’adda suna kai komo tsakanin yankunan da ke kan iyaka da kasar da kuma Turkiya, inda suk shigowa kai tsaye a cikin kasar tare da mara baya daga Turkiya.
Babu wani lamari da yake a boye dangane da yadda gwamnatin kasar Turkiya take daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasashen Iraki da sham kamar take kuma bayar cda mafaka a gare su a cikin kasarta, domin cimma wasu burika na siyasa.
3332091