IQNA

Gangami A Kasashen Duniya Domin Nuna Goyon Baya Ga Ayatollah Nimr

23:14 - July 26, 2015
Lambar Labari: 3335535
Bangaren kasa da kasa, masu fafutkar rajin kare hakkin bil adama a kasashen duniya sun gudanar da jerin gwano domin nuna goyon baya ga Sheikh Baqgher Nimr tare da jan kunnen mahukuntan Saudiyya a kansa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sknemer.com cewa, a yau dubban mutane da ke rajin kare hakkin bil adama a kasashen duniya daban-daban sun gudanar da jerin gwano domin nuna goyon bayansu ga Ayatollah Sheikh Baqgher Nimr da mahukuntan saudiyya ke tsare da shi.
Daruruwan mutane a kasar Saudiyya ne suka gudanar da zanga-zanga da kuma wasu daga cikin kasashen duniya, da suka hada da Faransa, Birtaniya, Amurka, Jamus, Australia, Canada, Spain, Holland, Switzerland, Ireland, Bahrain, Iran, New Ziland, da kuma Keshmir, don nuna rashin amincewarsu da hukumcin kisan da wata kotu ta yanke ma fitaccen malamin na shia na kasar Sheikh Nimr Bakir al-Nimr.
Rahotanni daga kasar sun ce mutanen sun fito ne bayan sallar Juma’a a yau din nan don nuna rashin amincewarsu da wannan hukumci da suka bayyana shi da cewa hukumci ne na zalunci da nuna wariya da mahukuntan Saudiyyan suka yanke wa wannan malamin da kuma sauran mutane din da aka kama su sakamakon fitowa zanga-zanga.
Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama dai sun yi Allah wadai da wannan hukumcin suna masu cewa mutanen da aka yanke wa hukumcin kisan, suna kananan yara ne a lokacin da aka kama su. ‘Yan Shi’an kasar Saudiyyan dai suna fuskantar takuri da nuna wariya daga wajen gwamnatin Saudiyyan.

 

3335407

Abubuwan Da Ya Shafa: Nimr
captcha