Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, shugaban kasar Maky Sal ne ya jagoranci bude zaman taron a birnin Dakar na kasar ta Senegal mai taken sulhu da addinin muslunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa bababr manufar taron dai ita ce bayyana ma al’umma matsayin addinin muslunci dangane da hankoron da wasu suke na bata sunansa idon duniya, duk kuwa da cewa shi addini na sulhu da zaman lafiya.
Taron ya samu halartar mutane da dama da suka hada da malamn addini da kuma wasu daga cikin masana na kasar, wadanda suke da makaloli da suka gabatar a gaban taron, da nufin kara yada wannan ilmantarwa ta addini da son zaman lafiya.
Muhamamd Kuraishi Ibrahim Nyas shi ne shugaban kungiyar Ansaruddin, ya kuma gabatar da jawabinsa a wurin, inda ya ja hankulan al’ummar msulunci baki daya da su zama cikin fadaka, dangane da kokarin da ake yin a baya sunan muslunci.
3336534