Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar PressTV cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi suka dangane da gina sabbin matsgunnai yahudawa yan kaka gida da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a cikin yankunan palastinawa.
Bayanin ya ce abbu wani abin da zai halasta ma Isra’ila abin da take yin a cin zarafin fararen hla a cikin yankunan palastinawa, musamman gina matsigunnan da take yi tare da rshe musu gidaje da kuma karbe musu filaye.
A bayanin an bayyana abin da gwamnatin yahudawa sahyuniya take da cewa ya sabawa dukkanin ka’idoji na kasa da kasa, tare da yin kira da ta gagaguata dakatar da hakan, tare da bin kaidoji na duniya wajen yin mu’amala da mutanen yankin.
Baya ga kasar ta Jamus akwai kasashen yammacin turai da dama da suka yi kakkausar suka wannan mataki na gwamnatin yahudawan Isra’ila na gina sabbin matsugunnan yahudawa yan kaka gida acikin yankunan palastinawa.
Daga shekara ta 1967 ya zuwa yanzu haramatacciyar kasar Isra’ial ta gina matsugunnai kimanin 120 a cikin wannan yanki da yakunshi dubban gidaje na yahudawa.
3336706