Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News Arabic cewa, a jiya kungiyar yan ta’addan ISIS ta dauki alhakin kai harin kan masallacin Abha na gundumar Asir a kudancin kasar Saudiyya na jami’an tsaro.
Jamii’an tsaro na kasar Saudiyya ne suka rasa rayukansu a yau a lokacin da wani mutum da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a cikin wani masallaci na jami'an tsaron kasar, daga ciki mutane 15 sun mutu wasu kimanin 20 kuma sun samu raunuka.
Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta yan ta’adda ta kai hari a wani masallaci na ‘yan sunna bayan ta kai irin hakan wasu yankuna na mabiya tafarkin iyalan gidan manzo wato shi’a a Kadih da kuma Qatif da ke gabacin kasar a lokutan baya.
Majiyoyin ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Saudiyyah sun ce mutumin ne ya tayar da bama-baman da ke jikinsa a cikin masallacin a garin Abha da ke cikin gundumar Asir a kudancin kasar, a lokacin da aka kai harin Muhammad Bin salaman dan sarkin kasar kuma ministan tsaronsa yana kasar Masar wajen bde gabar ruwa ta Suwiz nan take ya juyo.
Kungiyar ‘yan ta’addan IS ta fitar da sanarwar cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da harin, kuma ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar ta Saudiyya, inda a halin yanzu suke kafirta hatta da mahukuntan na Saudiyyah.
Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Saudiyyah ta nuna damuwa matuka dangane da abin da ka iya zuwa ya dawo sakamakon shiga cikin kungiyoyin ta’addanci matasan kasar ke yi, inda su ne suka fi a yawa a tsakanin ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare a cikin kasashen Syria da Iraki, wanda kuma wasu daga cikinsu suna komawa gida, bayan samun gogewa kan ayyukan ta’addanci.