IQNA

Wani Pastor Na Addinin Kirista Ya Karbi Addinin Muslunci A Najeriya

20:35 - August 07, 2015
Lambar Labari: 3339771
Bangaren kasa da kasa, wani malamin addinin kirista kuma jagoran wata majami’a a Najeriya ya karbi addinin muslunci.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OnIslam cewa, Adekonel Afolabi wani malamin addinin kirista ne kuma jagoran wata majami’a  a Najeriya ya karbi addinin muslunci bayan gina majami’arsa tun kimanin shekaru biyar da suka gabata.

Afolabi ya ce ya yi mafarki inda ya ga wani mutum a cikin mafarki, yana sanye da fararen tufafi yana sheda masa cewa, addinin muslunci shi kadai ne addinin tsira, kuma duk mai son tsira dole ne ya bi addinin muslunci.

Wannan mutm dan shekaru 45 da haihuwa yana zaune a garin Adi Ekiti a cikin jahar Ekiti, kuma ya gina majami’arsa tun shekaru 5 da suka gabata inda yake koyar da addinin kiristanci a wurin.

Tun kimanin shekaru 25 da suka gabata Afolabi yake halartar ayyukan ibada na addinin kirista, yana mai tsarkake niyyrsa ta hanyar bin awwanan addini, wanda kuma daga karshe Allah madaukain sarki ya shirye shi.

Yanzu haka dai ya mayar da majami’ar tasa masallaci inda ake karatun kur’ani da kuma koyar da addinin muslunci, yayin da wasu daga cikin mabiyansa suke karbar muslunci a masallacin nasa.

Najeriya dai tana da mutane miliyan 140 a tsohohuwar kididdiga, kuma kashi 5 musulmi ne, kashi 40 kuma mabiya addinin kirista ne.

3339259

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha