IQNA

An Girmama Wasu Mata Mahardata Kur’ani mai Tsarki A Kasar UAE

19:37 - August 11, 2015
Lambar Labari: 3341291
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da bayar horon kur’ani mai tsarki mai taken Kur’ani (Nufi daya hanya daya) tare da halartar mata 270 a cibiyar Darul-Bir da ke birnin Dubai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na GToday cewa, an gudanar da wannan horo ne tare da halatar jami’a daga ma’aikatar kula da harkokin addini da al’adu ta kasar.

Babbar cibiyar kula da harkokin mata da kuma bangaren tarbiya gami da malaman addini da kuma malaman kur’ani gami da masana kan harkokin addini na kasar sun halarci wanann zaman a karshe domin girmama matan da suka halarci horon.

Wadanda suka samu wannan horo an basu takardun sheda na kammala karatun, haka nan kuma za su yi amd\fani da shedar domin koyarwa  awasu makarntu kur’ani mai tsarkia  kasar.

A wurin taron an gabatr da karatun kur’ani mai tsarki, kamar yadda kuma aka gabatar da bayanai dangane da matsayin wannan littafi mai tsarki.

A cikin shirin an samu halartar mata daga shekaru 8 har zuwa shekaru 67 na haihuwa.

3341019

Abubuwan Da Ya Shafa: uae
captcha