IQNA

Muhammad Jawad zarif Ya Gana Da Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah

23:56 - August 12, 2015
Lambar Labari: 3341758
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Iran a daren jiya ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, Muhamamd Jawad Zarif ya gana da Sayyid Hassan Nasrullah tare da tabo batun tsaro da ya shafi kasar da ma yankin baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif wannan it ace ziyararsa ta farko a kasar ta Lebanon ya gana da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar ta Lebanon da suka hada da firayi ministan kasar Lebanon Tamam Salam dangane da muhimman lamurra da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.

A lokacin ganawar tasu Muhammad Jawad Zarif ya babbayan cewa Iran tana goyon bayan dukkanin matakan da Lebanon take dauke domin tabbatar da tsaron iyakokinta, kamar yadda kuma ya jadda cewa Iran za ta ci gaba da taimaka ma kasar ta Lebanon a dukkanin bangarori.

 

A nasa bangaren firayi ministan kasar ta Lebanon ya yaba wa kasar ta Iran dangane da yadda take taimaka ma kasar Lebanon. Bayan kammala tattaunawar tasu Zarif ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah.

Duk da cewa wannan it ace ziyara ta farko da ya kai kasar ta Lebanon, amma ya yi ganawa mai tsawo tare da bababr sakataren kungiyar Hizbullah, kamar yadda ya tafiya ta kasance tare da rakiyar Husain Amir Abdulahiyan, da kuma jakadan Iran a Lebanon Muhammad Fath Ali.
Bangaren ‘yan siyasa na 14 ga watan March sun bayyana bayanan na Zarif da cewa na hankali da girmama juna.
3341475

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha