IQNA

Matsalolin Duniyar Musulmi A Yau Na Da Aalaka Ne Da Hannaye Na Ketare

23:47 - August 15, 2015
Lambar Labari: 3344506
Bangaren kasa da kasa, hakikanin gaskiyar lamari dangane da matsalolin duniyar musulmi a yau a hakan yana da alaka ne kai tsaye da hannayen da kungiyoyin liken asiri na ketare suke da shi a cikin musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Khalil Hamdan daya daga cikin kussoshin kungiyar Amal a kasar Lebanon ya fadi a yau a gaban bababn taron cibiyar Ahlul bait (AS) ta duniya a karo na 6 a birnin Tehran cewa, matsalolin da duniya musulmi ke fuskantya a halin yanzu ba na ‘yan salafiyya ne ba kawai, akwai hannun kasashen ketare ta hanyar yin amfani da kungiyoyin liken asirinsu a cikin kasashen musulmi da na larabawa.

Khalil Hamdan wanda shi ne ya wakilci shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon a taron ya bayyana cewa, a hlin yanzu muna ganin ayyukan ta’addanci a cikin kasashen musulmi, kamar yadda muke ganin ta’addancin yahudawan Isra’ila, a lokaci guda suna amfana kuma da ta’addancin cikin muslmi, wanda kuma Isra’a ce kawai ke amfana da hakan ba, hata ma kasashen da suke da hannu wajen samar da ‘yan ta’addan.

Haka nan kuma ya bayar da misali kan yadda kasshen ketare da suka amfana da ta’addanci suka matsa lamba kan jamhuriyar muslunci ta Iran tare da bayyana abin da suka yin a saka mata takunkumi na karya tattalin arziki akan bankunanta da saurans da cewa duk naui ne na ta’addanci.

An bude taron ne nay au tare da jawabin shekh Hassan Rauhani shugaban kasar Iran, tare da halartar baki kimanin 700 daga kasashen duniya 130, da ska hada da malamai da kuma masana, kuma taron zai ci gaba da guda har zuwa kwanaki 4 a nan gaba.

3344322

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha