IQNA

Dubban Mutanen Bahrain Sun Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar ‘Yancin Kasa

23:57 - August 15, 2015
Lambar Labari: 3344507
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane a kasar Bahrain sun gudanar da jerin gwano da gangami a dukkanin sassa na kasar domin tunawa da ranar ‘yancin kasa da kuma jadda bkatarsu ta neman dimukradiia a kasar.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz na Manama Post cewa, a jiya mutane a kasar Bahrain sun gudanar da jerin gwano da zanga-zanga duk da matakan tsaro a dukkanin sassa na kasar domin tunawa da ranar ‘yancin kasa da kuma jadda bukatarsu ta neman dimukradiya da kuma hakkokinsu na ‘yan kasa.

An dai gudanar da wannan zanga-zanga da gangami a yankin Deraz tare da jadda cewa ba za a taba barin gwagwarmay neman hakkokin na al’ummar kasar ba, musamman ma wadanda suka shafi neman a kafa tsari na adalci da zai hada dukaknin bangarori na kasa baki daya, kamar yadda a ka jadda wajabcin sakin shugaban jam’iyyar Al-Wefaq Sheikh Ali salman.

Haka nan a sauran yankna na kasar an gudanar da irin wannan gangami, duk kuwa da cewa jami’an tsaron masarautar kasar sun dauki tsauraran matakai domin tabbatar da cewa ba a bar jama’a kasar sun gudanar da wanann gangami kamar yadda aka shirya.

Jami’an tsaroa  cikin kayan sarki sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da harsasan roba domin tarwatsa dubban jama’a da suka nufi bababn dandalin na Lu’alu’a wanda ya zama wani wuri na musamman da ke nuna alama ta neman sauyi na siyasa a kasar ta hanyar lumana.

Jam’iyyun siyasa na kasar Bahrain sun mayar da dandalin Lu’a lu’a a matsayin wurin tunawa da yunkurinsu na watan Fabrairun 2011 tare da kiran jama’a da su taru a wannan dandali.

3343076









Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha