IQNA

Malam Sunnah A Lebanon Sun Goyo Bayan A Hukunta Dan Ta’addan Salafiyya

20:14 - August 18, 2015
Lambar Labari: 3345843
Bangaren kasa da kasa, wasu daga malaman sunna a kasar Lebanon sun nuna cikakken goyon bayansu ga daukar matakin hukunta Ahmad Assir da sauran yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alamanar cewa, wasu daga cikin fitattun mamlan sunna a kasar ta Lebanon sun bukaci da a yanke hukuncin da ya dace da Ahmad Assir, tare da ladabtar da duk wani wanda ya aikata ta’addanci a kasar koma wane ne.
Sheikh Ahmad Kattan daya daga cikin fitattun malaman sunna a kasar Lebanon kuma shugaban kungiyar Kauluna wal Amal ya bayyana jin dadinsa da kuma godiyarsa ga babban jami’in kula da harkokin tsaron cikin gida Abbas Ibrahim wanda ya sanar da kame dan ta’adda Ahamd Assir.
Jami'an tsaron kasar Lebanon sun cafke dan ta'adda Ahmad Assir, wanda ke da hannu a hare-haren bama-bamai da dama da ake kaiwa a cikin Lebanon, kamar yadda yake da hannu wajen sace tare da kashe sojoji da jami'an tsaron Lebanon da dama.

 

Sheikh Hssam Ilani shi ma daya daga cikin malaman Lebanon kuma limamin masallacin Gufran na yankin Saida ya sheda cewa, abin da ya faru bababn abin farin ciki ne ga dukkanin al’ummar kasar, kuma hakan yana kara tabbatarwa yan ta’adda cewa komai nisan jifa kasa za dawo, da sannu za su shiga hannu domin fuskantar sharia.

Jami’an tsaron na Lebanon sun sanar da kame shi ne a a jiya Asabar a filin tashin jiragen sama na Beirut yana kokarin fita daga kasar da fasfo na jabu zuwa birnin Alkahira na kasar Masar.

tun bayan cafke shi dai har yanzu jami’an tsaron na Lebanon ba su yi wani karin haske kan halin da ake ciki ba dangane da lamarin nasa.

 

Ahmad Assir shi ne ya kafa kungiyar Salafiyya a kasar Lebanon, wanda daga bisani kuma ya dauki makamai yana yaki da gwamnatin kasar Lebanon tare da tayar da bama-bamai tare da kashe sojojin Lebanon da dama, kamar yadda kuma yake da alaka ta kud da kud da kungiyoyin ‘yan ta’adda na IS da Nusraf ront.
3345038

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha