Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na On Islam cewa, General Sani Kuka Sheka Usman daya daga cikin manyan jami’an sojin Najeriya ya bayyana cewa, abin takaici ne yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suke da’awar hankoron kafa daular addinin muslunci duk kuwa da cewa da dama daga cikinsu bas u karanta Fatiha.
Rundunar Tsaron Najeriya ta yi kakkausar suka kan yadda mayakan boko haram ke aikata ta’addanci a sunan musulinci alhali ba su sanar komai ba dangane da Addinin musulunci.
A wata sanarwa da ya sanya hanu a kankanta, kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce babban abinda ya basu mamaki shine mafi yawan mayakan kungiyar boko haram da suka kame a dajin sambisa ko fatiha ba su iya karantawa ba.
Ya ce a yayin da suka kame wasu sansani da kuma guraren da ake horas da mayakan boko haram a dajin Sambisa, sun samu makamai da wasu na’urorin aikin soja gami da wasu ababen fashewa, saidai abin mamaki babu wani abu dake nuna alamar addinin musulinci kamar su kur’ani da littatafai,
Jami’in ya ce wananna abu shi ke kara tabbatar da cewa sojojin haya ne aka dauka domin bata sunan musulmi da musulinci, wadanda bas u da alaka da addini domin kuwa bas u san shi ba.
‘yan ta’addan na Boko Haram dai suna cewa yin karatu na zamani wato Boko a cikin harshen Hausa haram ne a wurinsu, bisa wanann hujja suke kai hari kan makarantu da cibiyoyin ilimi suna kashe jama’a.
Har yanzu haka dai akwai daruruwan mutane fararen hula da mayakan kungiyar ta Boko Haram suke rike da su suna yin garkuwa da su a wurinsu, wanda hakan ko shakka babu ya bata sunan muslunci a idon duniya baki daya.
Kashi 55 daga cikin mutane Najeriya dai mabiya addinin muslunci ne, yayin da kuma 40 mabiya addinin kirista ne.