Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarai da hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, jaridar da ake bugawa a cikin harshen faransanci a kasar Senegal LE SOLEIL fitowar ranar Juma’a ta iya shara da da irin tarukan da aka fara gudanarwa kan fim din Muhammad Rasullah (SAW) na Majid Majidi a birnin Tehran da sauran larduna na jamhuriyar muslunci da cewa, wannan fim na kokarin bayyana hakikanin surar muslunci da manzon da kuma kalubalantar bayyana muslunciu da cewa addini na rashin rahama.
Babbar manufar shirya wannan fim na Muhammad Rasulullah (SAW) ita ce kare manzon Allah daga duk wani kokari na batunci da wasu ke yi, wanda kuma an kashe kimanin dala miliyan 40 wajen shirya wannan fim, wanda aka fara nunawa agidajen sinima, kuma hakan ya nuna muhimmancin fina-finan Iran a kafofin yada labaran yammacin nahiyar Afirka.
3354417