IQNA

23:50 - September 08, 2015
Lambar Labari: 3360642
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya kirayi kasashen nahiyar turai da su zama masu ‘yancin siyasa, maimakon zama ‘yan amshin shata ga siyasar Amurka.


Jagoran juyin Islama a Iran Ayatollah Sayyid Khamenei ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Austria Heinz Fischer da ke ziyara a Tehran, inda ya ce ; "Babban aibu ne ga wasu kasashen nahiyar turai yadda suka zama  'yan amshin shata ido rufe ga siyasar Amurka."

A nasa bangaren shugaban kasar ta Austria Heinz Fischer ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da ziyarar tasa a Iran, wadda ita ce ta farko da wani shugaban kasa daga yammacin turai ya kawo kasar Iran a cikin shekaru 11 da suka gabata, ya kuma jadda cewa Vienna za ta kara fadada alaka a fuskokin cinikayya da bunkasa tattalin arziki tare da Tehran.

Tun jiya ne dai shugaban na Austria tare da tawagarsa da ta kunshi mutane 240 suka fara ziyarar aiki a Tehran.

Shugaban kasar Austria ya fara ziyarar aiki a nan Iran a yau talata. A dazu da safe ne shugaban kasar ta Austria Heinz Fischer ya iso Tehran tare da tawagar da ta ke rufa masa baya, domin ganawa da manyan jami’an gwamnatin Iran. Shugaba Fischer ya gana da shugaban kasar Iran inda su ka tattauna muhimman batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu.

A taron manema labaru na hadin guiwa da su ka gabatar a dazu, shugaban kasar Iran ya tabo batutuwan da su ka shafi siyasar gabas ta tsakiya musamman kasar siri da ya bayyana cewa; Babu wata kasar waje wacce ta ke da hakkin zabarwa kasar makomarta. Shugaban na Kasar Iran, ya kuma bayyana cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran s shirye ta ke ta zauna kan teburin tattaunawa da kowane bangare domin dawo da tsaro a cikin kasar Syria.

Dangane da alaka Iran da Austria, shugaban na Iran ya ce; Alakar kasashen biyu dadaddiya ce ta daruruwan shekaru. Har ila yau, shugaban na Iran ya jinjinawa Austria saboda bakuncin tattaunawar Nukiliyar Iran da ta dauka. A nashi gefen, shugaban kasar ta Austria, ya ce; Kasarsa za ta bunkasa cinikayya da Iran, domin ganin ta kai euro miliyan dari uku kafin karshen wannan shekara.    

3360629

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: