IQNA

An Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Burundi

23:38 - September 09, 2015
Lambar Labari: 3361030
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a kasar Burundi tare da halartar mahardata 58 daga sassa na kasar.


Kamfanin dillani9cn labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, an gudanar da wannan gasar ne tare dataimakon babbar majalisar mabiya addinin muslunci a bangaren koyon likitanci na jami’ar Bujumbura babban birnin kasar tare da halartar masu gasa 85 da suka hada da maza da mata.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gasar ne a bangarori biyar da suka hada hardar kur’ni baki daya, izhi 15, sai kuma izihi 7, sai kuma izihi 5, d akuma bangaren izihi 3, tare da halartar alkalai guda hudu.

Haka nan kuma an bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa, tare da halartar Fadel Juma’a mamba a majalisar dattijan kasar da kuma Abdulwahab Yahya Sarari, wanda shi ma maba ne na babbar kungiyar mahardata kur’ani ta duniya.

Kasar Burundi dai tana tsakiya Afirka ne kuma Bujumbura shi ne babban birninta, tana tsakanin wata babbar korama da ke tsakanin kasashen Uganda, Congo, da kuma Rwanda gami da Tanzania.

3360728

Abubuwan Da Ya Shafa: burundi
captcha