IQNA

Kungiyoyin Kasashen Kasashen Musulmi Sun Yi Na’am Da Kafa Tutar Palastinu A UN

21:59 - September 13, 2015
Lambar Labari: 3362170
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kuma ISESCO sun na’am da matakin kafa tutar palastinu a majalisar dinkin duniya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na OIC cewa, kungiyar ta yaba da matakin kafa tutar palastinu a majalisar dinkin duniya, tare da fatan hakan ya zama masomi na amincewa da hakkokin palastinawa da kuma daga wannan tuta a sauran ofishosi na majalisar dinkin duniya.

Majalisar dinkin duniya ta amince da kafa tutar Palastinu a matsayin ‘yar kallo a shadkotarta dake birnin Nework na kasar Amurka da kuma dukkanin daftarinta dake duniya, inda ta ce a nan gaba za a kada kuri’ar amincewa da wannan bukata ko kuma akasin haka.kasashen duniya da dama wadanda suke a matsayin manba na Majalisar sun bayyana amincewarsu da wannan kudiri, saidai kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu.



Mai magana da yawun Ma’aikatar harakokin wajen kasar ya bayyana wannan kudiri a matsayin abinda ba za su taba amincewa da shi ba , shi kuma wakilin haratamciyar kasa a majalisar dinkin duniya ya bayyana wannan kudiri a matsayin  cewa Palastinawa na son yin amfani da majalisar dinkin duniya ta hanyar da ba ta dace ba.



Kafin gudanar da zaben, masu sharhin kan harakokin siyasa na ganin cewa wannan kudiri zai samu amincewar manbobin fiye da kasashe dari da hamsin ne suka kada kura’a,inda kasashe dari da sha tara daga cikinsu  suka kada kuri’ar amincewa, kasashen takwas kuma suka kuri’ar rashin amincewa, yayin da kasashe arba’in da biyar  kuma suka kada kuri’ar ba ruwansu, bayan kada kuri’ar amincewar.



A cikin shekaru sittin da bakwai da suka gabata haramtacciyar kasa ta aikata ta’addanci daban –daban a kan al’ummar Palastinu da suka hada da kisan kare dangi, kwace masu gidajensu-mamaye yankuna masu yawa daga cikin kasar su, killacewa da sauransu, amma duk da haka al’umma Palastinu na ci gaba da kwada juriya gami da hakuri domin cimma manufofin da suka sanya a gaba na kwato kasar su daga mamayar  ba.



3361832

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha