IQNA

Shekhul Azahar Ya Musunta Cewa Wurin Da Ake Kira Hubbaren Imam Ali (AS) Ba A Nan Yake Ba

23:52 - September 14, 2015
Lambar Labari: 3362571
Bangaren kasa da kasa, Ahmad tayyib babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana cewa wurin da aka rufe Imam Ali (AS) ba shi ne wurin da ake kira hubbarensa ba a halin yanzu.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shfaquna cewa Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wurin da aka rufe Imam Ali (AS) ba shi ne wurin da ake kira hubbarensa ba a halin yanzu da aka sani.

Ya ci gaba da cewa a lokacin da da Imam Ali (AS) ya rasu ana cikin fitintinu wanda hakan ya sanya ya bayar da umarni aka rufe shi a cikin dare a asirce, kuma an rufe shi a cikin makanbartar Wadi salam da ke cikin birnin Najaf mai alfarma, saboda hakan wurin da ake kira hubbarensa ba kabarinsa ba ne.

Ayyib ya ce mutane suna ziyarsa a wani bangare na wannan makabarta ne da sunan suna ziyartar hubbaensa alhali ba a nan ne kamar yadda yake rayawa.

Ya yi ishara da cewa Salaman Farsi da kuma Huzaifah Yamani daga cikin sahabban manzon Allah an rufe su a wurin, amma saboda ambaliyar ruwan Dajla, kabrukansu sun bude kuma an dauke su zuwa wani wuri na daban.

3362418

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha