Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Aktue cewa, kungiyar ISESCO kula da harkokin yada aladun uslunci ta duniya ta yi kakakusar suka dangane da keta alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan sahyuniya ke yi a cikin masallaci maialfarma.
A yau ne shugaban gwamnatin yahudawa ya ziyarci masallacin Al-aqsa a dai dai lokacinda ake cika kwanaki hudu sojojin haramtacciyar domin tsokanar mabiya addinin muslinci, kasar suke ta fafatawa da Palasdinawa wadanda suke son kare masallacin daga shiga yahudawan cikinsa.
Zuwansa cikin masallacin dai yana iya ingiza Palasdinawa su shiga borin da ake kira Intifada kamar yadda ya faru a ranar ashirin ga satumba dubu biyu a lokacinda tsohon da ya gabace shi yay yi.
Rahotannin da suke fituwa daga birnin Qudus suna nuna cewa a wannan karon yahudawan suna son kwace masallacin ne kwatkwata su kuma maida shi karkashin ikonsu, don yahudawan sahyohniyya su fara shiga masallacin don yin ibadarsu.
Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi ne suka kai harin tare da daruruwan ‘yan sanda Isra’ila a cikin kayan sarki da suke ba su kariya, ‘yan sandan Isra’ila sun shiga cikin masallacin, inda lakada wa masallata duka, tare da tarwatsa su da barkonon tsohuwa, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane fiye da dari.
3363100